in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shin allurar rigakafin kamuwa da cutar mura tana da amfani ga kananan yara?
2016-01-04 16:18:24 cri

Ko yi wa kananan yara allurar rigakafin kamuwa da cutar mura yana iya ba su kariya yadda ya kamata? Kwanan baya, masu nazari daga kasar Japan sun gano cewa, bayan da aka yiwa yara wannan allura, akwai bambanci a tsakanin kananan yara wadanda shekarunsu suka sha bamban a duniya ta fuskar ba da kariya yadda ya kamata.

Alal misali, ko da yake an yi allurar ga kananan yara wadanda shekarunsu suka kai watanni 6 zuwa watanni 11, da kuma wadanda shekarunsu suka kai 13 zuwa 15 a duniya, amma ba a iya kare su daga kamuwa da cutar ta mura ba.

Masu nazari daga jami'ar Keio ta Japan, sun gudanar da wani bincike kan kananan yara fiye da dubu 4 da dari 7, wadanda shekarunsu suka wuce watanni 6 amma ba su kai 15 da haihuwa ba, sa'an nan zafin jikinsu ya taba zarce digiri 38, kana sun taba samun jinya a asibitoci guda 22, daga watan Nuwambar shekarar 2013 zuwa watan Maris na shekarar 2014.

Masu nazarin sun yi bincike kan ko kwayoyin cutar mura sun taba kama wadannan kananan yara, da kuma ko an taba yin musu allurar rigakafin kamuwa da cutar ko a'a. Sun kuma tantance yadda mabambantan alluran rigakafin kamuwa da cutar mura suka kare kananan yara daga kamuwa da cutar mura mai nau'in A da B, a kokarin tabbatar da amfanin alluran.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, bayan da aka yi musu alluran, ba a iya kare jariran da shekarunsu suka wuce watanni 6 amma ba su kai watanni 11 a duniya ba daga kamuwa da cutar mura mai nau'in A ba. Sa'an nan kuma, ba a iya kare 'yan makarantar midil da shekarunsu suka wuce 13 amma ba su kai 15 a duniya ba daga kamuwa da cutar mura mai nau'in A da B ba.

Duk da haka, yin allurar rigakafin yana iya kare sauran kananan yara daga kamuwa da cutar mura mai nau'in A yadda ya kamata, musamman ma cutar mura mai nau'in A na H1N1.

Har kullum ana fatan yin allurar rigakafin kamuwa da cutar mura zai iya hana cutar yin kamari. Bayan da masu nazarin na Japan suka yi wannan bincike, sun gano cewa, galibi dai yin allurar rigakafin cutar mura yana iya hana cutar mai nau'in A ta yi kamari, amma abun bakin ciki shi ne bai iya hana cutar mura mai nau'in B tasiri yadda ake fata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China