Waiwaye adon tafiya. Bisa tarishi, sabuwar kasar Sin ta zamani ta kafa huldar diplomasiyya da kasashenmu na Afirka ne a tsakanin shekarun 1960-2015, kuma sabuwar nahiyar Sin ta zamani da kasashenmu na Afirka masu tasowa inda kasar Sin da kawayenta kasashenmu na Afirka suka cimma manyan matakan samun bunkasuwa bisa lumana da zaman karko bisa manyan tsare-tsare da hadin gwiwa, lamarin da ya bude wasu muhimman sabbin shafika bisa manyan matakan cimma burin juna bisa samun zarafin kyautatawa juna ingiza zaman lafiya da karuwar habakar tattalin arziki. Agaskiya, kasar Sin ta shigo kasashenmu na Afirka ne dan samar da muhimmiyar moriya ga dukkan kasashenmu na Afirka masu tasowa ta yadda kasashenmu na Afirka za su samu zarafin farfadowa daga muguwar illar da kasashen yan mulkin mallaka turawa daga kasashen nahiyar turai wayanda suka cutar da al'ummar kasashenmu na Afirka. Amma zuwa yanzu, kasashenmu na Afirka sun samu kyautatuwar rayuwa da habakar tattalin arziki bisa taimakon sabuwar kasar Sin a nahiyarmu ta Afirka. Muna godiya ta masamman ga mashuran shugabannin kasar sin bisa yadda suka nuna gwazo da himma wajen tsamo kasashenmu na Afirka daga kangin wahalhalun da turawa yan mulkin mallaka suka tsunduma nahiyarmu ta Afirka.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.