in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abubuwan sha masu dauke da sinadarin Caffeine na iya rage saurin girman kwakwalwar matasa
2015-12-20 12:31:19 cri

Asusun nazarin harkokin kimiyya na kasar Sweden ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a kwanan baya cewa, shan abubuwa masu dauke da sinadarin Caffeine zai iya rage saurin girman kwakwalwar matasa.

Sanarwar ta ce, masu nazari a asibitin kula yara na Zurich sun baiwa beraye masu kwanaki 30 a duniya wato daidai da kuriciyar 'yan Adam kofi na kwanaki 5 a jere. Masu nazarin sun gano cewa, idan an kwatanta da takwarorinsu wadanda suka sha ruwa zalla a lokacin gudanar da nazarin, berayen da suka sha kofin ba su yi barci sosai ba, tsawon lokacin da suka kwashe wajen yin barci mai nauyi ya ragu kwarai da gaske, sannan kuma saurin girman kwakwalwarsu shi ma ya ragu.

Jagoran nazarin ya yi karin bayani da cewa, kamar yadda beraye da sauran dabbobi masu shayar da nono, mu ma 'yan Adam mu kan kwashe dogon lokaci muna yin barci mai nauyi a lokacin yarantakarmu. Sannan a lokacin kuruciyarmu kuma, muna son yin barci sosai. Kwakwalwarmu tana iya girma cikin sauri yadda ya kamata a lokacin da muke yin barci mai nauyi. Wasu matasa suna sha'awar shan abubuwa masu dauke da sinadarin Caffeine, domin su wartsake, amma sannu a hankali sinadarin Caffeine kan hana mutum barci, kuma rashin issasshen barci na iya kawo illa ga girman kwakwalwar matasa.

Bayan haka kuma, masu nazari daga kasar Jamus sun gudanar da wani nazari na daban mai ban sha'awa, inda suka gano cewa, idan yara ba su samu isasshen barci sosai da dare ba, hakika kashegari ba za su iya karatu yadda ya kamata ba.

Masu nazarin sun kwashe makonni 4 suna gudanar da wannan nazari kan yara 110 'yan kasar Jamus wadanda shekarunsu suka wuce 8 amma ba su kai 12 ba. Sun gano cewa, idan har yaran suka samu isasshen barci da dare, to, kashegari, musamman ma da safe, kwakwalwarsu za ta fi daukar karatu kwarai da gaske. Amma idan tsawon barcin da ya kamata su samu ya ragu ko kuma ya wuce wadda suka saba yi da dare, to, yadda kwakwalwarsu za ta dauki karatun zai kasa na kashegari.

Bayan haka kuma, ga yaran da ba su sami maki mai kyau a karatu ba, abu mai muhimmanci a gare su shi ne su samu isasshen barci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China