in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin kwai na iya taimaka wa jikin yara karbar kwai
2015-12-12 13:06:17 cri

Kwai yana daya daga cikin wasu nau'o'in abinci da jikin wasu yara ke ki. A yawancin lokaci, likita kan bai wa irin wadannan yara shawarar kada su ci abincin da jikinsu ke ki. Amma wani sabon nazari da aka yi a kasar Amurka ya shaida cewa, a bar yaran da jikinsu ya ke kin kwai su sha ruwan kwai sannu a hankali, inda ake sa ido sosai kan yawan ruwan kwai da suke sha, hakan a cewar nazarin zai iya taimaka wa jikin yaran karbar kwai daga baya.

Masu ilimin kimiyya suna ganin cewa, a cikin tsawon lokaci, a bar mutane su ci abincin da jikinsu yake ki sannu a hankali, ana sa ido sosai kan yawan abincin da suke ci, hakan zai iya taimaka wa jikinsu karbar abincin da jikinsu ya ke ki a baya.

Shehun malami Wesley Burks, daga cibiyar kiwon lafiya ta jami'ar Duke ta kasar Amurka, shi ne ya jagoranci wannan nazari, inda masu nazarin suka raba yara 55 zuwa rukunoni 2, wato wadanda jikinsu ya ke kin kwai, kuma shekarunsu ke tsakanin 5 zuwa 11 a duniya. A cikin rukuni na A, yara 40 suna cin garin furotin kadan wanda aka sarrafa daga kwai a ko wace rana. Yara 15 na rukunin B kuma, suna cin garin masara a ko wace rana.

Bayan watanni 22, a cikin rukuni na A, jikin yara 30 ya iya karbar garin furotin na kwai da yawansa ya kai giram 10, yayin da dukkan yara na rukuni na B ba su iya cin garin furotin na kwai ba. Bayan dukkan yaran sun daina cin garin furotin har tsawon makonni 6, wasu 18 daga cikin yaran 30, jikinsu ya iya karbar garin furotin na kwai da yawansa ya kai giram 10 da kuma wani kwai.

Shehun malami Burks ya ce, bisa sakamakon nazarin, ana ganin yiwuwar taimakawa jikin mutum karbar wasu nau'o'in abinci. Sulusin yaran da ke cikin nazarin, jikinsu bai ci gaba da kin kwai ba.

Shehun malama Stacie Jones daga jami'ar Arkansas tana ganin cewa, taimakawa jikin yara karbar kwai yana iya sassauta damuwar iyayensu. Saboda iyayen kan nuna babbar damuwa, ganin cewa cin kwai yana iya halaka yaransu a makaranta ko a gidajen da suka ziyarta, idan ba su kula ba, suka ci kwai.

Amma duk da haka shehun malami Daniel Rotrosen daga cibiyar nazarin cuta mai yaduwa, da kuma yadda jikin mutane ya ke kin wasu abubuwa dake kasar Amurka, ya yi nuni da cewa ko da yake ana iya ganin yiwuwar taimakawa jikin mutum karbar wasu nau'o'in abinci bisa sakamakon wannan nazari, amma ana nan ana ci gaba da jarraba sakamakon nazarin, ana kuma bukatar kara gudanar da nazari a wannan fanni. Ya kuma yi gargadi da cewa, kada a gudanar da wannan nazari a gida. Saboda idan ba a maida hankali sosai ba, za a iya cin karo da mummunan sakamako. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China