lafiya1537.m4a
|
A kwanakin baya, wasu masu ilimin likitanci na kasashen Birtaniya da Amurka, sun bayyana cewa nazarce-nazarce da dama sun shaida cewa, ga wadanda suke da koshin lafiya, yawancin abinci ko abin sha masu dauke da bitamin da ma'addinai da ke gina jiki, ba su da amfani gare su wajen kiyaye lafiyarsu, don haka kwashe dogon lokaci wajen cinsu, bata kudi ne ke nan.
Masana daga kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Johns Hopkins dake Amurka, da na jami'ar Warwick dake Birtaniya, sun fidda wani sharhi dake cewa, ga baligai wadanda suke da koshin lafiya, yawancin abinci ko abin sha masu dauke da bitamin da ma'addinai ba su da amfani gare su, watakila ma su iya haifar musu da illa. Don haka bai kamata a ci su domin yin rigakafin kamuwa da cuttuttukan dake addabar mutum sannu a hankali ba.
Wadannan masana sun gudanar da nazarce-nazarce guda 3. A cikin nazari na farko, bayan da suka yi binciken lafiyar mutane fiye da dubu 400, sun gano cewa, babu wata shaida da ke nuni da cewa, cin abinci ko abin sha masu dauke da bitamin da ma'addinai, yana iya rage yawan mutuwar mutane, ko kuma rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da ciwon kansa.
A cikin nazari na biyu da uku kuma, an gano cewa babu wata shaida, ta cewa cin abinci ko abin sha masu dauke da bitamin da ma'addinai a ko wace rana, yana iya karewa tsoffi tabarbarewar kwarewar su, ta fahimta ko tunani. Haka kuma, wadannan abinci ko abin sha ba su da amfani wajen yin rigakafin sake abkuwar ciwon zuciya.
Har ma sakamakon wasu nazarce-nazarce ya yi gargadi da cewa, cin abinci ko abin sha da yawa masu dauke da bitamin E, da sinadarin da ake samu daga karas kan kara barazanar mutuwa.
Kowa ya san cewa, bitamin da ma'addinai na da matukar muhimmanci wajen kiyaye lafiya. Wasu ma na bukatar kara shigar da su ta wasu hanyoyi, baya ga ta hanyar cin abinci. Alal misali, a kasashe da dama, ana bai wa masu juna biyu shawarar rika shan folic Acid, don kada jaririn da ke cikinsu ya gamu da wata nakasa a lokacin da yake girma.
Amma masanan suna ganin cewa, a Amurka da wasu kasashe, yawancin wadanda suke ci ko sha abinci ko abin sha masu dauke da bitamin da ma'addinai, suna iya samun isassun sinadaran bitamin da ma'addinai daga abinci na yau da kullum. Don haka bai kamata su kara shan wani magani mai dauke da su da ke gina jiki ba. (Tasallah Yuan)