in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari shirin 'Allah daya gari bamban'
2015-09-20 12:12:31 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing, kamar yadda na ke lafiya a nan birnin Kano. Bayan haka,na samu sauraron sabon shirin ku na 'Allah daya gari bamban' na jiya Jumu'a 18 ga watan Satumba, kuma hakika, na ji dadin wannan shiri da malama Lubabatu Lei ta zanta da Maman Ada dangane da littafin da ya rubuta mai suna 'Haduwa ta da Sinawa'.

Ko shakka babu, bisa tattaunawar da na saurara a jiya dangane da abubuwan da littafin ya kunsa, na fahimci cewa akwai muhimman batutuwa masu ma'ana dangane da zaman rayuwar baki a kasar Sin musamman baki da suka zo daga nahiyar Afirka. Wato littafin zai zama haske ga wanda bai taba zuwa kasar Sin ba wajen fahimtar halayyar Sinawa ta yin haba-haba da baki, da kuma yadda baki ke samun rayuwa cikin 'yanci da walwala a lokacin da suke gudanar da kasuwanci ko rayuwar aiki a fadin kasar Sin. Daga cikin irin kyakkyawar mu'amalar da ke gudana tsakanin Maman Ada da abokansa Sinawa, wani dandali da Maman Ada da Sinawan ke haduwa don yin rawa da yammaci ya fi burge ni, domin kamar yadda na gani shi kadai ne bakar fata a cikin su, hakika ina iya tuna wannan lokaci yayin ziyara ta a kasar Sin kimanin shekarun biyar da suka gabata.

A daidai wannan gaba, bai zo min da wani mamakin jin cewa, gidan rediyon kasar Sin CRI ya kuduri aniyar wallafa wannan littafi mai suna 'Haduwa ta da Sinawa' kyauta a madadin shi marubucin wato malam Maman Ada, domin wannan batu na daya daga cikin abubuwan da littafin ya kunsa, wato karamcin da Sinawa ke gwadawa ga duk wani abokin mu'amalarsu. A ra'ayi na, gayyatar da na samu zuwa kasar Sin ba tare da biyan ko Kobo ba, na daya daga cikin karamcin al'ummar Sinawa, kuma hakan na daga cikin sauran dalilai da ke jan hankalin dimbin baki daga kasashen ketare dake sha'awar zuwa yin aiki ko kasuwanci a kasar ta Sin.

Ina fatan sashen Hausa na CRI zai dauki nauyin raba wannan littafi ga masu sauraro bayan an kammala aikin wallafa shi, domin masu sauraro da ba su taba jefa kafarsu a kasar Sin ba za su samu ilimi da fahimtar hakikanin dabi'a da halayya mai kyau ta Sinawa, da kuma yadda baki ke gudanar da rayuwa cikin 'yanci da walwala a kasar Sin.

Na gode,

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China