lafiya1516.m4a
|
Shekara da shekaru masu ilmin kimiyya na ganin cewa, matsalar kiba ta zama ruwan dare ne a duk duniya, sakamakon sauyawar hanyar rayuwar mutane, da hanyar da suke bi wajen gudanar da ayyukan sun a yau da kullum.
Sakamakon ci gaban da kimiyya da fasaha suka samar na sanyawa mutane su dade suna zaune a kan kujera, da makamantan ta ba tare da motsawa ko kadan ba, wanda hakan sannu a hankali ke sanya kiba taruwa a jikunan mutane.
Amma sabanin wannan tunani, abun mamaki shi ne ba da dadewa ba an gano cewa ba wannan ne dalilin aukuwar kiba ba!
A baya bayan nan wasu masu nazari daga wasu jami'o'in kasashen Amurka, da Tanzaniya, da Birtaniya sun hada kai wajen gudanar da wani bincike, inda suka zabi wasu mutane a wurare daban daban, suka bukace su da su sanya wani madauri mai dauke da tsarin binciken wurare na duk duniya mai aiki da tauraron dan Adam wato GPS a wuyan hannunsu, inda suka bi diddigi, da kuma rubuta abubuwan da wadannan mutane suke yi a ko wace rana, sa'an nan suka yi gwaji kan fitsarinsu, domin kara sanin yadda wadannan mutane suke amfani da karfin jikin su a ko wane lokaci.
A karshe dai masu nazarin sun gano cewa, babu babban bambancin tsakanin yawan karfin da ake amfani da shi tsakanin wadanda suke aiki a ofis a New York, da kuma wadanda suke farauta a dazuka da filayen dake yankin Gabashin Afirka.
Haka kuma masu nazarin sun gano cewa, a wurare masu ci gaban tattalin arziki, kamar kasashen Turai da Arewacin Amurka, komai bambancin yawan motsa jiki da mutane suke yi, yawan calorie da suke konawa a ko wace rana na kusan yi daidai da na juna. Wato a iya cewa, komai wahalar da ka sha yayin da kake motsa jiki, hakan kadai ba zai sanya ka rage kiba mai yawa ba.
Duk da haka masu nazarin sun gano cewa, manoman da suke rayuwa ta hanyar da gargajiya ta kaka-kakaninsu a kasar Bolivia, su na dan kara kone calorie, in an kwatanta su da wadanda suke yin farauta. Wannan ya nuna cewa, yin aikin noma ba shi da sauki sam.
Duk dai da wannan sakamako na masu nazari dake nuna cewa motsa jiki ba shi da amfani kwarai wajen taimakawa mutane su rage kiba, a daya hannun motsa jikin na iya inganta lafiyar mutane, lamarin da ya fi muhimmanci kwarai da gaske ga rayuwar dan Adam.
Ga alama, idan kana son rage kiba, to, ya fi kyau ka mai da hankali kan kayyade yawan calorie da ke cikin abincin da ka kan ci, saboda ba bu wata sahihiyar hanya da za ka iya bi wajen kone calorie da ka ke tarawa a jiki, bayan ka shigar da su jikin na ka ta hanyar cin abinci.(Tasallah Yuan)