Kasashen Sin da India manyan kasashe ne da suke samun bunkasuwar tattalin arziki cikin hanzari kuma kasashen 2 suna da manufufi iri daya da juna wajen ingiza huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu tsakanin kasashen 2. Kana kasar Sin da India suna martaba makwabtakar dake tsakaninsu da juna, al'amarin da ya kara hadin kansu a matsayinsu na manyan kasashe a nahiyar Asia. Kana kuma, kasashen 2 suna da matsayi na kolokuwa a duniya wajen yawan al'umma a duniya inda kasar Sin ta zama ta daya a duniya wajen yawan al'umma yayinda makwabciyarta India ta zama ta 2 a duniya. Dan haka, wannan ziyara da shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping zai fara a kasar India a ranar laraba 17 ga watan satumban shekarar 2014, za ta kara habbaka hulda diplomasiyya da cinikaiya da bunkasa aiyukan jiragen kasa da samun bunkasuwa tare da kuma kawo ci gaba a tsakanin kasar Sin da India ta fuskar tsaro da dai sauransu. Babu shakka, ganawar Firaministan kasar India mr. Narendra Modi da shugaban kasar Sin Xi za ta kara kawo bunkasuwar kasashen yadda yakamata kana shugabannin kasashen 2 za su kara ingiza huldar dake tsakaninsu ta fannin tattalin arziki yayinda za su yi musayar ra'ayi a tsakaninsu cikin yakini da amuncewar juna.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.