in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaunannun wakilan hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyyar kwaminis ta Sin sun gana da 'yan jarida
2012-11-15 15:41:01 cri

A ranar Alhamis 15 ga watan nan da safe ne sabon babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping da sauran zaunannun wakilan hukumar harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya, wato Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan da kuma Zhang Gaoli, sun gana da 'yan jarida na gida dana waje a babban dakin taron jama'ar kasar Sin.

Xi Jinping ya ce, burin dukkan mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma fatan dukkan jama'ar kasar shine sa kaimi wajen kokarin gudanar da ayyukan cigaba da kuma daukar nauyi dake kan su.

Kana Xi Jinping ya nuna cewa, kamata ya yi zaunannun wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar su hada kan dukkan membobin jam'iyyar da kuma jama'ar kasar, su kuma cigaba da yin kokari wajen raya kasa, bude tunanin jama'a, bude kofa da yin kwaskwarima, inganta karfin bunkasa zamantakewar al'umma, warware matsalolin jama'a, da kuma bin hanyar samun wadata tare. Hakazalika ya kamata su yi kokari tare da dukkan membobin jam'iyyar wajen raya jam'iyyar, warware matsaloli, gyara kuskure, da kuma yin mu'amala da fararen hula don tabbatar da jam'iyyar ta jagoranci dukkan kasar, a fagen bunkasa Sin mai halayen musamman na gurguzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China