in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tabbatar da samun karuwar hatsi cikin shekaru 9 a jere
2012-10-30 10:13:20 cri

Ma'aikatar lura da sha'anin noma ta kasar Sin ta sanar a jiya Talata 23 ga wata cewa, ko shakka babu kasar za ta samu karin yawan hatsi a lokacin kakar bana, hakan kuma na tabbatar da samun karuwar hatsi cikin shekaru 9 da suka wuce a jere.

An ce, ya zuwa ranar 22 ga wata, yawan hatsin da aka girba a kasar ta Sin, ya kai murabba'in eka miliyan 64.73, wanda ya kai kashi 83 cikin dari bisa na dukkan hatsi da aka shuka baki daya. Idan aka yi kirgar hatsin da aka samu a yanayin zafi da shinkafa da aka samu, to an riga an girba kashi 90% na hatsin da aka shuka a shekarar da muke ciki, kuma ana kyautata zaton cewa, yawan hatsin da za a samu a bana zai kai sabon matsayi a tarihin kasar.

Wani jami'in ma'aikatar lura da sha'anin noma ta kasar Sin ya bayyana cewa, muhimman dalilan da suka sa aka samu karuwar hatsi a cikin shekaru 9 da suka wuce, sun hada da yanayi na bana, da ya zo da karin amfani, kana da kyautatuwar manufofi, fasahohi, da matakan da aka dauka na magance bala'u.

A yanzu haka ana karshen aikin girbin hatsi na yanayin kaka, saboda haka ma'aikatar sha'anin noma ta kasar Sin ta bukaci mahukuntan wurare daban daban, da su kara himma wajen aiki, domin samun cikakkiyar nasara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China