logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwarorinsa na Afirka ta kudu da Senegal

2024-09-01 20:04:44 CMG Hausa

A yau Lahadi ne mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Afirka ta kudu Ronald Lamola, da ta kasar Senegal Yassine Fall, wadanda suka iso kasar Sin gabanin taron FOCAC na bana da za a bude nan da ‘yan kwanaki.

Yayin zantawarsa da mista Lamola, jami’an biyu sun nazarci sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka ta kudu a fannoni da dama, sun kuma bayyana aniyarsu ta fadada hadin gwiwa a bangarori kamar na raya tattalin arziki, da cinikayyar zuba jari, da bunkasa ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da nufin samar da karin gajiya ga al’ummun kasashen biyu. (Saminu Alhassan)