in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawayen Sudan sun bukaci a sake fasalin tsaro a kasar
2020-01-06 10:23:32 cri
Tsagin kungiyar 'yan tawayen Sudan na SPLM-N, dake karkashin Malik Agar, ya bukaci gwamnatin kasar ta amince da sake tsarin tsaro da shugabanci.

Yasir Armani, mataimakin shugaban kungiyar 'yan tawayen, ya ce sun gabatar da kudurin ga sabuwar gwamnatin riko dake karkashin Firaminista Abdalla Hamdok, don fara aiwatar da garambawul ga tsarin tsaro da shugabanci, da nufin taimakawa wajen daidaita tattalin arzikin kasar mai rauni.

Yasir Armani ya bayyana yayin taron tattaunawar zaman lafiya a birnin Juba cewa, idan ba a sake fasalin bangaren tsaro ba, ba yadda za a yi a shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar. Haka kuma ba za a cimma samar da mulkin demokradiyya da tabbatuwar tsaro a kasar ba.

Ya ce kungiyarsu ta kuma bukaci gwamnatin ta samar da shirye-shiryen da ake bukata da za su bada damar shigar da wasu mayaka daga yankin Southern Blue Nile.

Yasir Armani, ya ce an samu ci gaba a tattaunawar zaman lafiyar kan batutuwa da dama. Inda ya ce, suna fatan dukkan kungiyoyi masu dauke da makamai za su amince da ra'ayinsu game da shirye-shiryen tsaron domin samun hadin kai, yana mai cewa, matakin zai kawo ci gaba a Sudan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China