in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ji karar fashewar bututun mai a jihar Lagos dake kudancin Najeriya
2019-07-04 19:23:13 cri
Wata majiyar rundunar 'yan sanda a jihar Lagos dake kudancin Najeriya, ta ce wani bututun mai ya yi bindiga a Alhamis din nan, kuma mai yiwuwa fashewar ta haifar da asarar rayuka.

Majiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, barayin mai ne suka haddasa fashewar, yayin da suke yunkurin dibar mai ta barauniyar hanya.

Wani jami'in hukumar kashe gobara a jihar, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, ana ci gaba da tattara alkaluman barnar da fashewar ta haifar.

A nasa tsokaci kuwa, wani mazaunin yankin da fashewar ta auku mai suna Oloruntoyin Kudus, ya ce ko shakka babu wasu mutane sun rasa rayukan su sakamakon gobara da ta tashi yayin aukuwar wannan lamari.

A daya bangaren kuma, wata kafar radio dake birnin na Lagos, ta bayyana rasuwar mutane biyu, wadanda suka kone kurmus, baya ga ababen hawa, da shaguna da gobarar ta lakume.

Wasu hotuna da suka kewaya kafofin sadarwa na yanar gizo, sun nuna wuta na ci ganga ganga, yayin da mutane ke gudun tsira da rayukan su daga yankin da fashewar ta auku. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China