Iran tana da matakai daban daban da za ta dauka, ciki har da batun ficewa daga yarjejeniyar da aka cimma, idan har an mayar da batun yarjejeniyar nukiliyar gaban kwamitin sulhun MDD, Behrouz Kamalvandi, kakakin hukumar sanya ido kan shirin makaman nukiliyar Iran, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Press TV.
Matakin da Tehran din za ta dauka na yin watsi da wasu daga cikin yarjejeniyoyin nukiliyar a cewarta hakan zai bada dama ga kasashen Turai karin lokaci wajen mutunta hakkokin dake wuyansu, kana hakan zai taimakawa yarjejeniyar ta kasa da kasa komawa aihin kan turbar da ta dace, in ji Kamalvandi.
Babbar manufar yarjejeniyar nukiliyar ta JCPOA shi ne, domin samun nasarar janye takunkumin da aka kakabawa kasar Iran domin baiwa kasar damar cin gajiya daga yarjejeniyar, in ji shi.
To sai dai kuma, har yanzu akwai matakai tsaurara duk da cewa Tehran din tana mutunta yarjejeniyar, kakakin na Iran ya bayyana hakan. (Ahmad Fagam)