Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya damu da rahotannin kai hare-hare ta sama kan cibiyoyin fararen hula a Syria.
Guterres ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya rabawa manema labarai. A ranar 5 ga watan Mayu ne, aka ba da rahoton kai hare-hare ta sama kan wasu cibiyoyin kiwon lafiya 3, adadin da ya karu zuwa cibiyoyin kiwon lafiya a kalla 7 ke nan da aka kai irin wadannan hare-hare tun a ranar 28 ga watan Afrilu.
Bugu da kari, an ba da rahotan kai irin wadannan hare-hare kan makarantu 9 a ranar 30 ga watan Afrilu, an kuma rufe wasu karin makarantu a galibin yankunan kasar, har sai baba ta gani.(Ibrahim)