Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce karfin zanga-zangar ranar 4 ga watan Mayu, ya karfafa buri da yakinin al'ummar Sinawa da ma kasar, na samun farfadowa.
Shugaban Xi Jinping, ya bayyana haka ne a yau Talata, yayin taron da aka yi don cikar zanga-zangar shekaru 100 da gudana.
Ya ce zanga-zangar muhimmin gangami ne na kishin kasa da juyin juya hali da matasa 'yan boko suka assasa, inda kuma al'ummar kasar daga ko wane bangare na rayuwa suka shiga aka dama da su wajen yaki da mulkin kama karya.
Xi Jinping ya ce ta kuma wayar da kai game da sabbin hanyoyin yada akidu da al'adu da kuma ilimi. (Fa'iza Mustapha)