in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitocin Sin sun isa Ghana domin gudanar da aiki kyauta
2019-04-29 10:05:06 cri

Tawagar jami'an lafiya Sinawa, sun gudanar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga ma'aikata 200 na kamfanin kayan karau na KEDA, a bangarorin lafiya daban daban, ciki har da acupunture da duba lafiyar ido.

Daya daga cikin ma'aikatan kamfanin mai suna Maurice, ya ce hankalinsa ya kwanta da gano cewa babu iyuwar ciwon hawan jini da yake da shi, zai kai shi ga kamuwa da wasu manyan cututtuka, bayan jerin gwaje-gwajen da likitocin Sinawa suka yi masa.

Ya ce, bai taba zaton zai samu irin wannan kulawar kwararrun a kyauta ba, yana cewa, kamar likitocin sun dauki asibiti ne kacokan sun kai masana'antarsu.

Har ilau, Maurice mai shekaru 23 ya ce, ana bukatar ayyukan likitocin, duba da cewa, har yanzu mutanen dake zaune a yankunan karkara na fuskantar matsalar biyan kudin kiwon lafiya saboda tsadarsa, duk kuwa da inshorar lafiya dake akwai.

A cewar Zhang Yong, daya daga cikin tawagar likitocin Sinawa, suna musu gwaje-gwajen da aka fi bukata kamar na hawan jini da sinadarin glucose, kuma da zarar sun ga akwai matsala, sai su tura su, su kara yin gwaje gwaje nan take.

An gudanar da dukkan ayyukan duba lafiyar a kamfanin a kan lokaci kuma a kyauta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China