Ana ganin cewa, ra'ayoyin da shugaban ya gabatar a jawabinsa dangane da kulla huldar abota a fannoni daban daban da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, za su taimaka ga inganta huldar kasa da kasa a bangarori da dama da kuma cin moriyar juna.
Bernadette Deka-Zulu, darektan zartaswa na cibiyar nazarin manufofi ta kwararrun kasar Zambia ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da wani sabon dandali na inganta harkokin ciniki da zuba jari a tsakanin kasa da kasa, kuma ta hanyar gina nau'o'in manyan ayyuka, an hade sassan duniya daban daban, matakin da ya samar wa kasashen Afirka damar yin ciniki da kasa da kasa. (Lubabatu)