Minista Ouaro ya bayyana cewa, Sin da Burkina Faso sun sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu cikin kasa dashekara daya, inda aka samu nasarori da dama karkashin hadin gwiwarsu. Ya ce a fannin bada ilmi, Sin ta gina makarantun firamare guda biyu ga kasar Burkina Faso a cikin gajeren lokaci, kana za ta kara gina makarantun firamare 100 a kasar, wannan ya shaida sahihanci da karfinsu a wannan fanni. Ya ce ya yi imani cewa, kasashen biyu za su ci gaba da yin kokari tare wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.
A nasa bangare, jakada Li Jian ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da yin kokarin kyautata yanayin bada ilmi na kasar da kuma sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu a wannan fanni. (Zainab)