in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya dama ce ta karfafa aminci tsakanin Botswana da Sin
2019-04-21 15:31:26 cri

Halartar taron hadin gwiwa ta kasa da kasa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya zai ba Botswana damar karfafa aminci da hadin gwiwa da kasar Sin.

Babban sakataren ma'aikatar sufuri da sadarwa na kasar Botswana Kabelo Ebineng, ya shaidawa manema labarai a birnin Gaborone kafin tashinsa zuwa kasar Sin cewa, kasar Sin da sauran bangarori, ciki har da Botswana, za su yi bitar nasarorin da aka cimma da kuma lalubo fannonin da suke son kara hadin gwiwa karkashin shawarar.

Ministar sufuri da sadarwa, Dorcas Makgato ce za ta wakilci kasar ta nahiyar Afrika, a taro na 2 da za a yi kan shawarar ziri daya da hanya daya, a nan birnin Beijing daga ranar 25 zuwa 27 ga watan nan na Afrilu.

Kabelo Ebineng, ya ce hadin gwiwa kan shawarar mataki ne da yake mayar da hankali kan kirkire-kirkiren abubuwa dake haifar da kyawawan sakamako, kuma bangarori daban-daban za su kara hadin gwiwa a matakai daban-daban da za su samar da sakamako mai matukar inganci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China