in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kwashe 'yan ci rani 163 daga Libya zuwa Niger
2019-04-20 15:23:42 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta ce ta kwashe 'yan cirani 163 daga Tripoli, babban birnin Libya, zuwa Niger, la'akari da rikicin da ake fama da shi a birnin Tripoli tsakanin dakarun gwamnati da rundunar soji dake da mazauni a gabashin kasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce jirgin da ya kwashe 'yan gudun hijirar 163 zuwa Niger, ya sauka lafiya da safiyar jiya Juma'a.

Ta kara da cewa, cikin kwanaki 10 da suka gabata, hukumar ta yi kokarin sauyawa 'yan ci rani 539 matsuguni, daga cibiyoyi daban-daban da ake tsugunar da su dake kusa da wuraren da ake yaki, ciki har da 'yan ci rani 179 na cibiyar Abu Selim dake kudancin kasar, yayin da ake tsaka da gwabza fada a yankin

Tun a farkon watan nan na Afrilu ne rundunar sojin ke kai farmaki da nufin kwace iko da birnin Tripoli daga hannun gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, kawo yanzu, fadan ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 200, da jikkata wasu sama da dubu tare da tilastawa dubban fararen hula tserewa daga gidajensu.

Rundunar sojin ta hada kai ne da gwamnatin gabashin kasar, duba da cewa kasar na fama da rarrabuwar kawuna sanadiyyar siyasa tsakanin gwamnatin gabashi da na yammacin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China