Songwe ta bayyana cewa, ta kuma tattauna da shugaba Biya game da yiwuwar kasar ta Kamaru na fadada fannonin tattalin arzikin kasar da zai kai bunkasar kaso 10 cikin 100, idan har ta shiga cikin yarjejeniyar cinikayyar.
Sai dai sanarwar fadar shugaban kasar, ba ta bayyana ko kasar Kamarun, daya daga cikin kasashen Afirka da suka sanya hannu kan yarjejenitar a shekarar da ta gabata, za ta shiga yarjejeniyar cinikayya ko a'a.
Ya zuwa yanzu, kasashen Afirka 22 ne, suka amince da yarjejeniyar, adadi mafi kankanta da ake bukata cikin kasashe mambobin AU 55 kafin amincewa da ita.(Ibrahim)