in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai harin bom a kasar Somaliya
2019-04-18 13:26:47 cri
Bangaren 'yan sanda na kasar Somaliya ya bayyana a jiya cewa, an kai harin bom da aka ajiye a cikin mota a birnin Mogadishu dake kasar a wannan rana, wanda ya haddasa mutuwar mutane 5 tare da raunatar mutane 5.

Mataimakin jami'in mai bada umurni na 'yan sanda na kasar Somaliya Hossain ya bayyana cewa, bom da aka ajiye a cikin wata mota ya fashe a kofar wani dakin cin abinci dake birnin Mogadishu a wannan rana. Ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa, mutane 4 sun mutu kuma mutane 5 sun ji rauni a sakamakon harin, watakila yawan mutanen da suka mutu zai karu.

Har zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin harin ba. amma manazarta sun yi hasashen cewa, kungiyar Al-shabaab ce ke kai hare-hare irin kamar hakan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China