Yayin taron manema labarai, Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD, ya ce tun bayan da mahaukaciyar guguwar Idai ta aukawa kasar Mozambique cikin tsakiyar watan Maris, hukumar samar da abinci ta MDD WFP, ta tallafawa mutane miliyan 1 da abinci a kasar.
A Zimbabwe kuwa, asusun bada agajin gaggawa ga yara na MDD, ya sanar da cewa, an fara bayar da rigakafin cutar kwalara na sha, ga mutane 488,000 a jiya Talata, a larduna biyu da guguwar ta fi shafa.
Sama da mutane 1,000 ne mahaukaciyar guguwar Idai da ruwan sama da ambaliya suka yi sanadin mutuwarsu. Har kawo yanzu, Dubban mutane ne ke bukatar agaji bayan aukuwar iftila'in.
Bankin duniya ya yi kiyasin cewa, kasashen da iftila'in ya shafa na bukatar dala biliyan 2 domin su farfado. (Fa'iza Mustapha)