in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dimbin tsuntsaye sun koma birnin Haikou sakamakon nasarar kiyaye yankunan fadama dake bakin tekun birnin
2019-04-16 11:49:41 cri

Birnin Haikou, babban birni ne na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, na daya daga cikin biranen dake samun nasara sosai a duk duniya wajen kiyaye yankunan fadama. Ba ma kawai yankunan fadama sun taka rawa sosai wajen kawata birnin da kuma yin ban ruwa ga gonaki ba, har ma sun sa birnin ya zama wani kyakkyawan wuri ga dabbobi da kifaye iri iri. A yankin Dongzhaigang, wato yankin dake bakin teku mafi kyan gani a birnin Haikou, akwai yankin kiyaye bishiyoyin bakin teku na Mangrove mafi girma a nan kasar Sin. A yankin, a kan ga kifaye iri iri da ba a iya ganinsu a sauran wurare ba. Ana farin cikin ganin kasancewar dimbin tsuntsaye iri iri. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

Bishiyoyin bakin teku na Mangrove da suke kasancewa kamar gandun daji a teku, bishiyoyi ne da suke kasancewa a yankunan bakin teku. A duk duniya, ire-iren bishiyoyin bakin teku na Mangrove sun kai 80, sannan kasar Sin tana da ire-irensu 37. A yankin kiyaye bishiyoyin bakin teku na Mangrove na yankin Dongzhaigang, ana iya ganinsu 37 gaba daya. Mr. Feng Erhui, injiniya mai nazarin kiyaye Mangrove a yankin, ya bayyana cewa, " A lokuta daban daban, akwai furannin bishiyoyin bakin teku na Mangrove iri daban daban da suke fitowa. A kowace rana, ruwan teku na dawowa sau biyu, sannan ya koma sau biyu. A wadannan lokuta, ana iya ganin kifaye iri iri. Sannan a lokacin dawowar ruwan teku, ana iya ganin dimbin bishiyoyin bakin teku na Mangrove da suke kasancewa kamar wani babban gandun daji a teku. A yankinmu, ire-iren tsuntsaye sun kai 214, wato sun kai fiye da kashi hamsin cikin dari bisa dukkan ire-iren tsuntsyen dake lardinmu."

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, ire-iren kananan dabbobin dake da kashin baya wadanda suke kasancewa a yankin fadama na Haikou sun kai 514, wato sun wuce kashi 22 cikin dari bisa na duk kasar Sin. Sannan ire-iren bishiyoyin dake cikin yankin fadama na birnin sun kai 439, wato sun wuce kashi 20 cikin dari bisa na duk kasar.

Yankin kiyaye bishiyoyin bakin teku na Mangrove na Dongzhaigang yana cikin sabon yankin Jiangdong na birnin Haikou, muhimmin yanki ne inda ake kafa "Unguwar gwajin yin cinikayya cikin 'yanci ta Hainan". Idan an kiyaye bishiyoyin bakin teku na Mangrove, wane tasiri zai kawo wa birnin Haikou? Mr. Lu Gang, shugaban cibiyar nazarin yankunan fadama ta Duotan ta birnin Haikou ya bayyana cewa, a kan yaba da bishiyoyin bakin teku na Mangrove cewa, su ne suke kasancewa kamar "masu gadin yankunan bakin teku", suna taka rawa sosai wajen rage karfin iska da igiyar ruwan teku, da kuma taimakawa kananan dabobin dake cikin teku a lokacin da suke haihuwar jariransu. Mr. Lu Gang yana mai cewa, "Da farko dai, suna taka rawa sosai wajen hana shigar da iska cikin birnin, da kuma inganta dam da aka gina a bakin teku. Sannan suna taka rawa wajen kiyaye yanayin muhalli. Bisa nazarin da aka yi, an ce, galibin dabbobin teku, da yawansu ya kai fiye da kashi 60 cikin dari suna dogara da bishiyoyin bakin teku na Mangrove, musamman a lokacin da suke kanana. Gandun bishiyoyin bakin teku na Mangrove su ne ke kasancewa kamar wurin renon jariran dabbobin teku. Bugu da kari, bishiyoyin bakin teku na Mangrove suna da muhimmanci sosai ga kokarin rage yawan sinadari na Carbon."

Yankin kiyaye bishiyoyin bakin teku na Mangrove na Dongzhaigang, ya kasance kamar wani misali ga ayyukan inganta yankunan fadama da gwamnatin birnin Haikou take yi cikin kwazo da himma. Yanzu fadin yankunan fadama dake birnin Haikou, ciki har da yankunan fadama dake bakin teku, da na kogunan ruwa da na tafkuna da kuma yankunan fadama da aka kafa, ya kai kusan hektoci dubu 30, wato ya kai kashi 12.7 cikin dari bisa dukkan yankunan birnin. Dalilin da ya sa aka samu wadannan yankunan fadama shi ne, a 'yan shekarun baya, gwamnatin birnin Haikou na mai da hankali sosai wajen farfadowa da kuma kiyaye yankunan fadama. Mr. Chen Song, shugaban cibiyar kiyaye yankunan fadama ta birnin Haikou yana mai cewa, "Da farko dai, mun gayyaci wasu shahararrun kwararru da suka zo birnin Haikou domin taimaka mana wajen tsara shirin kiyaye yankunan fadama. Sannan mun kafa dokokin kiyaye yankunan fadama a majalisar kafa dokoki ta birninmu. Daga shekarar 2014 zuwa yanzu, mun riga mun kafa dokoki 4 masu alaka da aikin kiyaye yankunan fadama, ana kuma aiwatar da su kamar yadda ya kamata. Bugu da kari, mun kafa wani kwamitin kwararru wadanda suka fito daga sassa daban daban na kasarmu, da kuma lardinmu, domin ba da shawarwari kan aikin kiyaye yankunan fadama." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China