Lu Kang ya ce, kawo yanzu, kasashe 16 dake yankin tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai, tare kuma da kasar Girka, sun rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar hadin-gwiwa a fannin "ziri daya da hanya daya", kana, Italiya da Luxembourg da wasu sauran kasashen Turai su ma sun daddale takardar bayani kan hadin-gwiwar shawarar "ziri daya da hanya daya" tare da kasar Sin.
Lu ya kara da cewa, za'a kaddamar da babban dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fuskar shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a karshen mako mai zuwa a Beijing, inda shugabannin kasashe daban-daban gami da wasu manyan wakilan nahiyar Turai za su hallara. Kasar Sin za ta gudanar da shawarwari kan matakan hadin-gwiwa da za ta dauka tare da bangarori daban-daban, ciki har da kasashen Turai, don bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda hadin-gwiwarsu za ta ci gaba da habaka ba tare da wata matsala ba.(Murtala Zhang)