in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kula da albarkatun man fetur a Nijeriya ya kawar da fargabar da ake game da karancin mai a kasar
2019-04-15 09:34:17 cri

Ministan kula da albarkatun man fetur na Nijeriya, Ibe Kachikwu, ya kawar da fargabar da al'ummar kasar mai arzikin man fetur ke yi, game da karancin man fetur a wasu sassan kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar, Ibe Kachikwu ya ce kasar ta wuce zamanin karancin man fetur, inda ya bukaci masu ababen hawa su daina sayen man saboda fargaba, yana mai tabbatar da cewa ana da isasshe a kasar.

Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito a ranar Asabar cewa, wasu birane na fama da karancin mai, bisa zargin wasu dillalai da kin dauko man daga rumbunan ajiya.

Kamfanin mai na kasar NNPC, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, yana da sama da lita biliyan 1 na mai a ajiye, inda yake kuma da karin wasu kwantainonin mai 48 dauke da lita miliyan 50 da aka ware ga watan Afrilu kadai.

Ya kara da cewa, babu bukatar sayen man da yawa ko boye shi saboda fargabar karancinsa.

Haka kuma, dilallan mai na kasar, sun ce nan bada dadewa ba, karancin man da ake fuskanta a wasu birane na kasar zai yi sauki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China