A rukuni na A, Masar mai masaukin baki, za ta fafata da kungiyar Leopards ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kungiyar Cranes ta Uganda da kuma Warriors ta kasar Zimbabwe.
Masar da Zimbabwe ne za su bude gasar ta AFCON na bana, wadda za a fara ranar 21 ga watan Yuni.
A rukunin B kuma, kungiyar Super Eagles ta Nijeriya za ta fafata da takwararta ta National Sily ta kasar Guinea da kuma Burundi da Madagascar, wadanda suka samu cancantar shiga gasar AFCON a karon farko.
Senagal kuma za ta barje gumi a Rukuni na C da kasashen Tanzania da Kenya da kungiyar Fennecs ta Aljeria. Yayin da rukunin D ya kunshi Morocco da Cote d'Ivoire da Afrika ta kudu da kuma Namibia.
Sai rukuni na E, inda Tunisia za ta kece raini da Eagles na Mali da Mauritania, wadanda suma suka shiga gasar a karon farko, sai kuma kasar Angola.
Kasar Kamaru kuma za ta kare kambunta ne da Black Stars ta Ghana da kasar Benin da kuma Guinea Bissau. (Fa'iza Mustapha)