An soma gasar ce a hukumance a ranar 28 ga watan Fabrairun bana, inda aka shafe wata guda ana tattara hotunan, baki daya an samu hotuna sama da 11,500 daga masu ziyartar shafin yanar gizo na kasashe da yankuna 47 dake kan hanyar "Ziri daya da hanya daya". A waje guda kuma, an samu labaru da hotuna masu burgewa da dama.
Bayan haka kuma, an jefa kuri'u a yanar gizo, don gayyatar masu ziyartar yanar gizo a duk fadin duniya su zabi hotunan da suka burge su, inda kimanin mutane dubu 750 suka shiga wannan shiri. (Bilkisu)