in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana martaba ma'aunin ingancin kaya na EU
2019-04-11 09:50:44 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana cewa, kasarsa za ta nace ga tsarin yin komai a bayyane yayin da take yin hadin gwiwa kan kayayyakin more rayuwar jama'a da kasashen kungiyar tarayyar Turai (EU) tare da martaba dokoki da ma'aunin ingancin kaya na kungiyar ta EU.

Li ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabar kasar Croatia Kolinda Grabar-Kitarovic, har ma ya mikawa shugabar gaisuwar shugaba Xi Jinping na kasar Sin.

Da yake karin haske kan alakar kasashen a fannin ababen more rayuwa, Li ya bayyana kudirin kasarsa, na ganin an kammala dukkan ayyukan da take gudanarwa bisa inganci, za kuma ta nace ga tsarin moriyar juna, da alakar moriyar juna da ta bai daya a wannan fanni.

Ya ce, a kullum kasashen Sin da Croatia, suna mutunta juna da rashin nunawa juna bambancin matsayi, bisa tushen samun moriyar juna, kana suna raya alakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Jami'in na kasar Sin ya ce, yayin taron shugabannin Sin da na EU karo na 21 da aka kammala, an amince cewa, ya kamata sassan biyu su zuba jari ga juna ba tare da nuna son kai ba, alakar da Sin da EUn ya dace su martaba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China