in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fassara na kasar Sin sun taimaka ga ayyukan ceto a yankunan dake fama da mahaukaciyar guguwar Idai a Mozambique
2019-04-09 15:01:35 cri

A cikin shirinmu na wannan mako, za mu gabatar muku da wani bayani game da yadda wasu masu fassara na kasar Sin suka yi kokarin bada taimako ga ayyukan ceto a kasar Mozambique, wadda ke fama da bala'in mahaukaciyar guguwa da ake kira Idai mai tsanani.

A kwanakin nan, wasu kasashen Afirka, ciki har da Mozambique, da Zimbabwe da Malawi, sun sha fama da matsanancin bala'in mahaukaciyar guguwa da ake kira Idai, inda a kasar Mozambique, kungiyar ma'aikatan ceto ta kasar Sin, ciki har da wasu mutanen dake jin yaren Portuguese suka nuna himma da kwazo wajen samar da tallafi ga mazauna wurin don tinkarar bala'in. Daga cikin wadannan mutane masu jin yaren Portuguese, akwai Sinawan da suka dade suna zama a Mozambique, akwai kuma matasa dake aiki a wurin na wani kankanin lokaci, har ma akwai wasu 'yan asalin Mozambique wadanda suka taba yin karatu a kasar Sin. Wadannan mutane sun shiga cikin yankunan da ake fama da bala'in mahaukaciyar guguwar tare da ma'aikatan ceto gami da likitoci, don bada tasu gudummawar, tare kuma da bada taimako wajen daidaita harkoki tare da gwamnatin kasar Mozambique.

Bayan da birnin Beira gami da yankin tsakiyar kasar Mozambique suka gamu da bala'in mahaukaciyar guguwar mai karfin gaske ta Idai, wani dan kasar Sin wanda ke zaune a kasar har na tsawon shekaru sama da goma Wang Shengjun yana matukar son bada nasa taimakon ga mutanen da suke da bukata. A matsayin wani kwararren mai fassara a yaren Portuguese, da ya samu labarin cewa ofishin jakadancin Sin dake Mozambique yana neman masu jin yaren, Wang ya gabatar da sunansa ba tare da bata lokaci ba, inda ya ce:

"Na zo na gani, don bada nawa taimako, saboda muna zaune tare da 'yan kasar Mozambique. Duk da cewa mu ba 'yan kasar bane, amma ina ganin muna da alhakin bada taimako. Ko da yake ba ni da kudi ko kuma kayan tallafi da yawa, amma ina da lokaci, ina so in taimaka musu."

Gu Zi'ang, wani ma'aikacin kamfanin kasar Sin ne wanda ke aiki a kasar Mozambique na tsawon shekaru hudu. Bayan aukuwar bala'in, Gu ya shiga yankin Beira dake fama da bala'in cikin mota daga inda yake aiki wato birnin Maxexe don halartar ayyukan sa-kai. Gu ya bayyana cewa:

"Ina alfahari da kaina saboda samun damar halartar ayyukan ceto a nan. Na tuka mota daga waje mai nisa zuwa nan, wato tsawon yini daya akan hanya. Ban ci abinci sosai ba, kuma ban yi barci sosai ba a wannan wuri, ba don komai ba sai don ina son in bada nawa taimakon. Na farko ina son taimakawa 'yan Mozambique, na biyu kuma ina son daga kwarjinin Sinawa a wajen."

Akwai masu jin yaren Portuguese guda takwas wadanda suka shiga ayyukan ceto na kungiyar samar da tallafi ta kasar Sin. Ayyukansu su ne, samar da agajin kiwon lafiya, da gudanar da bincike kan annobar da ka iya kunno kai a yankuna masu fama da bala'in, da dai sauran wasu ayyukan ceto da dama. Wani dan kasuwa matashin kasar Sin mai suna Li Shuai, wanda ke aiki a birnin Nampula na kasar Mozambique, sau da dama ya je yankuna masu fama da bala'in mahaukaciyar guguwa mai tsanani don bada ceto. Li Shuai ya ce, zama wani mai aikin sa-kai muhimmin abu ne da ba zai taba mantawa ba a duk rayuwarsa, kuma ba ya jin tsoron komai a yayin da yake taimakawa mutanen Afirka. Li ya ce:

"Abun da ya fi burge ni shine, wata rana na je bada ceto a wani wuri mai suna Lamego, mai tazarar kilomita kimanin 80 da birnin Beira. Da na shiga wata harabar daki, na ga wasu gawarwaki 38 suna wari kwarai da gaske. Nine mutum na farko da na sauka daga mota, sai naje na tuntubi shugabannin wurin, don fahimtar yadda zamu gudanar da ayyukanmu. Amma bayan na sauka daga mota, sai warin gawarwakin ya mayar dani motar, kila ma ba zan sake gamuwa da irin wannan mummunan hali ba a duk rayuwata. Ni kaina na yi shekaru da dama ina kasuwanci a Afirka, inda na samu kudin shiga da dama. Ina matukar godiya ga nahiyar Afirka, don haka ina so in yi iyakacin kokarina don taimakawa wannan nahiya."

Bala'in mahaukaciyar guguwa ta Idai ya yi babbar hasara da ambaliyar ruwa ga birnin Beira gami da yankunan dake kewayensa, inda suka fuskanci babban hadarin yaduwar cututtuka ta hanyar ruwa, har ma an samu bullar cutar kwalara a wasu wurare. Ko da yake ma'aikatan kiwon lafiya sun samar da kayan rigakafi ga masu aikin sa-kai, amma suna fuskantar babban hadarin kamuwa da cututtukan yayin da suke kusantar marasa lafiya. Yayin da yake zantawa da wakilinmu game da damuwarsa kan kamuwa da cututtuka masu yaduwa a lokacin da yake tallafawa mutanen da bala'in ya shafa, Wang Shengjun ya bayyana cewa:

"A ganina yayin da ake gudanar da ayyukan ceto, na riga na manta da komai, ban damu ba ko akwai kayan rigakafi ko kuma babu. Aiki kawai nake yi. Na dukufa ka'in da na'in wajen gudanar da ayyukan ceto, da taimakawa sauran mutane."

Deng Yuren, wani matashin kasar Sin ne mai shekaru 20 da wani abu, wanda ya tashi daga birnin Cuamba dake arewa maso yammacin kasar Mozambique zuwa yankunan dake fama da bala'in mahaukaciyar guguwar Idai don samar da taimako. Deng Yuren, dan asalin birnin Guangyuan na lardin Sichuan ne wanda ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba ya samu taimako gami da tallafin da aka ba shi a lokacin aukuwar iftila'in girgizar kasa. Deng ya ce, yana alfahari sosai kan ayyukan ceton da Sinawa suka yi a kasar Mozambique, har ma yana alfahari sosai da ganin cewa shi dan kasar Sin ne, inda ya ce:

"A yayin aukuwar bala'in girgizar kasa mai karfin gaske a gundumar Wenchuan dake lardin Sichuan a shekara ta 2008, na tuna cewa an yi bala'in zabtarewar kasa a garinmu, inda ma'aikatan ceto da dama suka zo don taimaka mana. Kasa da mako guda, kamar kwana hudu ko biyar, an kawo mana kayan tallafi. Ni karamin yaro ne a wancan lokaci, ban yi tunani sosai ba, ban san yaya suka yi don kawo mana abinci da abun sha kasa da mako guda bayan aukuwar bala'in ba. Ina jin kunyar fadin hakan, amma a ganina wannan kauna ce ga kasarmu, ina alfahari sosai saboda ni mutumin kasar Sin ne. Idan ka zo nan, zaka iya fahimta cewa, idan wata kasa bata da karfi, jama'arta zasu sha wahala sosai."

Daga cikin mutane masu aikin sa-kai, akwai kuma wata 'yar kasar Mozambique wadda ke iya magana da harshen Sinanci sosai. Sunanta Angelica Sitoe, wadda ta taba karatu har na tsawon shekaru shida a kasar Sin. Ta bayyana cewa, irin kwazon aikin da likitocin kasar Sin suka yi na tallafawa mutanen da bala'in mahaukaciyar guguwar Idai ya ritsa da su, ya burge ta kwarai da gaske. A cewarta, likitocin kasar Sin ba su nuna wani bambanci ko kadan ba ga mutanen da bala'in ya shafa, har ma sun yi duk wani kokarinsu na taimaka musu. Angelica Sitoe ta ce:

"Likitocin kasar Sin sun kula da mu sosai, wato ba su nuna bambanci ko kadan ba ga mutanenmu dake fama da bala'in Idai a Mozambique da marasa lafiya na kasar Sin. Sun zo wurinmu don canja mana magani da kansu, babu wani bambanci kamar yadda na gani a kasar Sin. Gaskiya ina matukar farin ciki. Ina godewa ayyukan ceto da ma'aikatan kasar Sin suka yi, inda suka zo nan don taimaka mana cikin himma da kwazo. Sukan yi min godiya, suna cewa sannu da aiki Angelica, amma ya kamata in nuna musu godiya, in gode musu saboda tallafin da suka baiwa 'yan uwana mutanen Mozambique. Mun gode!"

Masu sauraro, bayan aukuwar bala'in mahaukaciyar guguwa mai karfin gaske da ake kira Idai a wasu kasashen Afirka, kasar Sin ta yi himma da kwazo wajen gudanar da ayyukan ceto, musamman a kasashen Mozambique da Zimbabwe da kuma Malawi. A Mozambique, tawagar masu aikin ceto na kasar Sin, sun bada gudunmuwar kayayyakin rage radadin iftila'i ga hukumomin lafiya na kasar Mozambique a Beira, babban birnin lardin Sofala da mahaukaciyar guguwar Idai ta fi daidaitawa.

Kayayyakin da darajarsu ta kai dala dubu 700 sun hada da, kayayyakin ceto da na asibiti da magunguna da gidajen tafi da gidanka da kuma tantuna.

Da yake godewa kasar Sin, darektan sashen aikin agajin kiwon lafiya na ma'aikatar lafiya ta kasar Ussene Issa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gudunmuwar ta kasar Sin, zata ragewa ma'aikatar lafiyar nauyin dake kanta na magance bukatun gaggawa da ake da su yanzu.

Ya ce ba gudunmuwa da suka karba kadai kasar Sin ta bayar ba, domin ta shiga ayyukan kula da wadanda mahaukaciyar guguwar ta rutsa da su da rabon abinci da ruwa. Ya kara da cewa, abun da suka samu daga kasar Sin shi ne goyon baya da karfin gwiwar da suke bukata.

Kididdigar da aka fitar a hukumance ta nuna cewa, mahaukaciyar guguwar Idai da ta aukawa yankin tsakiyar Mozambique a ranar 14 ga watan Maris da daddare, ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 518 tare da lalata gidaje 59,910 da hanyoyin ruwa da na tsaftar muhalli.

A yanzu haka, tawagar masu aikin sa-kai dake bada agaji ta kasar Sin ta riga ta bar kasar Mozambique, bayan da ta kammala aikin bada agaji cikin nasara ga wadanda mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta yiwa barna, yayin aikinsu a kasar, masu aikin sa kai na kasar Sin sun samar da ceton jinya ga masu bukata, tare kuma da tantance hadarin masifar, domin kubutar da masu fama da masifar daga mawuyacin yanayi. Adadin marasa lafiya da suka samu taimakon masu aikin bada agajin kasar ta Sin ya kai 3337, fadin wuraren da suka tsabtace ya kai muraba'in mita dubu 330.8, kana sun samar da abinci da magunguna da ruwa ga masu fama da iftila'i a kasar sama da dubu daya cikin gaggawa.

Babban jagoran ofishin kula da harkokin jin kai na MDD dake Mozambique Sebastian Rhodes Atampa ya bayyana cewa, tawagar bada agajin kasar Sin da kungiyoyin MDD suna gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu lami lafiya, kwazon aikin tawagar kasar Sin ya burge shi matuka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China