in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin bunkasa sabon tattalin arzikin birnin Beijing
2019-04-03 12:14:05 cri

A lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arziki mai inganci, ana ganin cewa, sabon tattalin arziki shi ne zai bunkasa tattalin arziki bisa sabon ilmin kimiyya da fasahohin zamani da aka kirkiro. Yanzu kasar Sin na kokarin hanzarta bunkasa irin wannan tattalin arziki lami lafiya ba tare da tangarda ba.

A lokacin da ake kokarin kyautata aikin tafiyar da harkokin yau da kullum a birnin Beijing, ana kuma sauyawa wasu tsoffin masana'antu matsuguni zuwa yankunan karkara ko sauran larduna, sannan ana kokarin rage karuwar masana'antun gargajiya wadanda mai yiyuwa za su gurbata muhalli ko kawo cunkoso ga birnin, ta yadda za a iya tabbatar da ganin birnin Beijing ya taka rawar kamar yadda babban birnin kasa zai taka, da kuma kare yanayin gargajiya na birnin, wato matsayinsa na tsohon babban birnin wasu dauloli na nan kasar Sin. Sabo da haka, gwamnatin birnin Beijing ta fitar da wata takarda, inda aka tabbatar da wasu sana'o'in da ba za a yarda da sake bunkasa su a yankin birnin ba, da kuma wasu sana'o'in da za a sa kaimi ga bunkasa su. A shekarar 2018 kadai, an rufe tsoffin masana'antu 656 wadanda suke samar da kayayyakin yau da kullum a nan Beijing. Game da yadda birnin Beijing yake kokarin tabbatar da ganin an bunkasa tattalin arziki mai inganci, madam Li Sufang, mataimakiyar direktan kwamitin gyare-gyare da ci gaban birnin Beijing, ta bayyana cewa, "A cikin shekaru 2 da suka gabata, an sauyawa tsoffin masana'antu 1307 matsuguni daga birnin Beijing da rufe kasuwanni da cibiyoyin sarafar kayayyaki wajen dari 5 bisa matakan rage masana'antu iri daya da aka kafa da dama, da rage yawan tsoffin masana'antun da ake da shirin kafawa da kuma rufe kofofin wasu masana'antu wadanda ba sa iya samun riba kamar yadda ake fata a kasuwa. Sakamakon haka, an samar da wasu filaye ga masana'antu ko kamfanoni wadanda suke bunkasa bisa fasahohin zamani da aka kirkiro. A cikin sabbin masana'antu da kamfanoni dubu dari 7 da aka kafa a shekarar 2018, yawan masana'antu da kamfanonin da suke neman ci gaba bisa bayanai da fasahohin zamani ya kai kashi 40 bisa dari, yawan jarin da suka yi rajista ya kai fiye da RMB yuan biliyan 730, wanda ya karu da 13.5% kwatankwacin bara. Yanzu gudummawar da kamfanonin ba da hidima bisa bayanai suka bayar ga karuwar tattalin arzikin birnin Beijing ta kai fiye da 60%."

Yankin kirkiro sabbin fasahohi na unguwar E9 yana gabashin birnin Beijing, a da, yanki ne na wata masana'antar samar da kayayyakin madara ta Beijing. A shekarar 2012, aka sauyawa wannan masana'anta matsuguni zuwa yankin raya masana'antu na Yinghai na gundumar Daxing dake karkarar Beijing. Sannan a shekarar 2014, wannan tsohon yanki ya sauya fasalinsa zuwa wani yankin raya masana'antu da kamfanonin kimiyya da fasaha ko na al'adu. Kawo yanzu, an kafa masana'antu da kamfanoni fiye da 80, ciki har da manyan kamfanoni 3.

A wannan yankin kirkiro sabbin fasahohi na E9, akwai wani kamfanin da ya mallaki ilmin kimiyya da fasahohin zamani da yake ba da hidimomi ga sauran kamfanoni da hukumomin gwamnati da bankuna da kamfanonin sadarwa kusan dubu 1. Madam Cui Jingjing, babbar jami'ar kamfanin ta bayyana cewa, "Muna ba da hidimomi ga wadanda suke amfani da hidimominmu bisa fasahohin tantance mutum bisa sautinsa da fuskarsa, da kuma ba da hidimomi bisa fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI ga ayyukan tantance masu neman rance daga bankuna. Ban da haka, muna ba da hidima bisa bayanan zamani dake hannun kamfaninmu ga kamfanoni a lokacin da suke kula da kuma tantance dukiyoyi da farashin kayayyakinsu da dai makamatansu. A nan kasar Sin, yawan matsakaita da kananan masana'antu da kamfanoni ya kai wajen miliyan 65, galibinsu ba sa iya samun goyon bayan hada-hadar kudi. Muna ba su hidimomi ta hanyar nazartar bayanai, ta yadda za a iya tabbatar da ganin sun samu kudaden da suke bukata da kuma rage yawan kudin tafiyar da harkokinsu da suke kashewa a kullum."

Birnin Beijing, wani tsohon birni ne da tarihinsa ya kai fiye da shekaru dubu 1, a lokacin da ake shiga sabon zamani, ana canja fuskarsa yana kuma zama wani birni dake cike da basira da kuma fasahohin zamani da aka kirkiro. Fadar Sarakuna dake cikin garin Beijing, an gina ta ne yau kusan shekaru 600 da suka gabata. A 'yan shekarun baya, bisa sabon halin da ake ciki, hukumar kula da ita ta kuma fitar da wasu kayayyakin tarihi, bisa fasahohin zamani, sannan bisa bukatun da masu yawon shakatawa suke da su wajen samun kayakyyakin zamani masu inganci a maimakon wasu kayayyakin nune-nunen al'adu kadai. Sakamakon irin wannan gyare-gyare, yawan kudin da hukumar kula da Fadar Sarakuna ta Beijing ta samu a shekarar 2017 ya kai RMB yuan biliyan 1.5 maimakon yuan miliyan 600 a shekarar 2013.

Yadda tattalin arzikin birnin Beijing yake samun bunkasa a 'yan shekarun baya, ya bayyana mana wani labari kan yadda ake sauya salon raya tattalin arziki a nan Beijing. A lokacin da ake yin watsi da tsoffin masana'antu wadanda ba su iya dacewa da sabon halin da ake ciki ba, ana kuma sa kaimi da raya tattalin arziki bisa fasahohin zamani da aka kirkiro. Sakamakon haka, birnin Beijing ya cimma burinsa na mayar da tattalin arziki irin na gargajiya ya zama sabon tattalin arziki, har ma ya samu ci gaba cikin sauri. Mr. Lin Keqing, mataimakin magajin birnin Beijing yana mai cewa, "A shekarar 2018, gudummmar da sabon tattalin arzikin ya bayar ga GDP na birnin ta kai kashi 33.2 cikin dari. Daga cikinsu, gudummawar da tattalin arzikin zamani, kamar na hada-hadar kudi, da ba da hidima bisa bayanai da ilmin kimiyya da fasahohin zamani ya bayar, ya kai kashi 67 cikin dari. Yanzu birnin Beijing ya kasance kamar wani abin misali ta fuskar kare al'adu da kuma bunkasa tattalin arzikin al'adu a duk fadin kasar Sin." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China