in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban kasar Sin a kasashen Italiya,Monaco da Faransa
2019-04-07 08:25:00 cri

Daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Maris ne, shugaba kasar Sin Xi Jinping ya gudanar ziyarar aiki a kasashen Italiya, Monaco da Faransa, ziyara ta farko zuwa ketare da shugaban kasar ya gudanar a wannan shekara. Kana ziyara irin ta ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai Italiya cikin shekaru 10.

Shugaba Xi ya ce alakar Sin da Italiya ta shafe tsawon lokaci cikin aminci duk kuwa da sauye-sauye da aka gamu da su a matakai na kasa da kasa, inda kasashen suka shafe shekaru 49 suna cudanya mai nagarta.

Bana shekaru 15 ke nan da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin Sin da Italiya. Kasar Italiya ta kasance zango na farko na ziyarar Xi a nahiyar Turai a wannan karo. Manazarta suna ganin cewa, shugaba Xi ya zabi kasashe uku na Turai a matsayin kasashen farko da ya kai ziyara a bana, hakan ya shaida cewa Sin ta mai da hankali sosai ga dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, kana birnin Rome ya zama wuri na farko da shugaba Xi ya kai ziyarar, wanda ya kara jawo hankalin duniya sosai.

Duk da kasancewar Monaco kasa ta biyu mafi kankanta a duniya, ta kulla alaka da kasar Sin kasa mafi yawan al'umma a duniya kana ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya a fannonin sadarwar zamani 5G da kamfanin Alipay da Huawei da yawon bude ido, kare muhalli da sauransu.

Haka zalika, shugaban kasar Sin ya nanata cewa, kasar Sin tana daukar nahiyar Turai da muhimmanci sosai, kuma ta dade tana kokarin raya huldar dake tsakaninta da kasashen Turai.

Kafin ya kammala ziyarar tasa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da dabarun kasar Sin kan yadda za a kawar da matsalar rashin nagartaccen mulki bisa ka'idojin nuna adalci da kawar da matsalar rashin amincewar juna bisa ka'idojin tattaunawa da kuma hakuri da juna. Bugu da kari, a kawar da matsalar rashin zaman lafiya ta hanyar tinkarar rikice-rikice cikin hadin gwiwa. Sannan, ya kamata a kawar da matsalar rashin ci gaba ta fannin moriyar juna da kuma neman nasara tare.

Raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a yayin ziyarar. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China