in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: A dauki matakai nan take don tinkarar kalubalen da ke gaban duniya
2019-03-27 15:20:35 cri

Jiya Talata 26 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron suka halarci bikin rufe taron dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Faransa kan tafiyar da harkokin kasa da kasa, taron da ya samu halartar shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Turai Jean Juncker bisa gayyatar da aka yi musu.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin mai lakabi "A ba da gudummawa don raya kyakkyawar duniyarmu" Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su dauki matakai ba tare da bata lokaci maimakon zura ido kawai, domin tinkarar manyan kalubaloli da duniya ke fuskanta, bisa la'akari da yadda makomar bil Adama ke hannunmu.

A yayin bikin rufe taron dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Faransa kan tafiyar da harkokin kasa da kasa da aka gudanar a birnin Paris jiya Talata, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya nuna cewa, a matsayinsu na muhimman bangarori masu fada a ji wajen tafiyar da harkokin duniya, Sin da Faransa suna da ra'ayi daya a siyasance da kyakkyawan tushen hadin kai a fannonin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, da tsayawa tsayin daka kan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da yin cinikayya maras shinge, da ma goyon bayan MDD wajen kara ba da tasirinta.

Shekaru biyu ke nan, yana nan Turai, Shugaba Xi ya taba yin tambayoyi yayin da yake jawabi a babbar hedkwatar MDD da ke Geneva, inda ya ce, "Me ke faruwa a duniya? Yaya ya kamata mu yi?". Yanzu haka, duniya na fuskantar babban sauyin da ba a taba ganin irinsa ba, ana kuma fuskantar matsalar rashin tabbas da kalobaloli daban daban. Game da hanyar da ta kamata dan Adam ya dauka don kara ci gabansa, Shugaba Xi ya bayyana dabarun kasar Sin, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su sauke nauyin da ke bisa wuyansu, da daukar matakai ba tare da bata lokaci ko zura ido kawai ba, bisa la'akari da yadda makomar bil Adama ke hannunmu. Xi yana mai cewa,

"Da farko dai, ya kamata a kiyaye adalci don kau da bambancin ra'ayi kan tafiyar da harkokin kasa da kasa. Wato a martaba ka'idojin shawarwari tare da ci gaba tare da ma more sakamako tare don raya makomar bil Adama ta bai daya yadda ya kamata. Na biyu kuma, ya kamata a nanata yin shawarwari da hakuri da juna, domin kau da bambancin ra'ayi kan amincewar juna. Wato a dora muhimmanci kan girmamawa da amincewa da juna, sa'an nan a kiyaye dabarun cimma muradu tare da martaba ka'idoji. Na uku shi ne, ya kamata a hada kai tare don kau da bambancin ra'ayi kan neman zaman lafiya. Wato a martaba sabon ra'ayin hadin kai don samar da tsaro mai dorewa daga dukkan fannoni, da warware rikici cikin lumana, da nuna adawa da sanya wasu kasashe cikin mawuyacin hali domin biyan bukatun kai. Na hudu kuma na karshe, ya kamata a kiyaye ra'ayin cin moriyar juna da samun nasara gaba daya domin kau da bambancin ra'ayin samun bunkasuwa. Wato a yi kokari don samun dauwamammen ci gaba, da bude kofa ga juna don samun nasara tare, da samun daidaito don amfana wa jama'a, ta yadda al'umomin kasa da kasa za su iya more sakamakon ci gaban dunkulewar tattalin arzikin duniya gu daya. Kasar Sin na maraba da kasa da kasa ciki har da Faransa da su shiga a dama da su cikin aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Haka kuma za mu ci gaba da yin kokarin yin shawarwari a tsakanin Sin da Turai ta fuskar zuba jari."

A nasa jawabin, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa, kiyaye tattaunawa a tsakanin Turai da Sin na da babban tasiri wajen kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama. Yadda kasar Sin ta samu saurin ci gaba, har ma ta fitar da mutane kimanin miliyan dari 8 daga fatara ya burge mutane sosai. Turai da Sin muhimman kusoshi ne a dandalin duniya, ya kamata su inganta amincewa da juna, da ma inziga hadin kansu ta hanyar tattaunawa. Shugaba Marcon ya kara da cewa,

"Shawarar 'Hanya daya da ziri daya' da Shugaba Xi ya gabatar na da babbar ma'ana, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman karko da ci gaba da zaman lumana tsakanin al'umomin duniya. Bangaren Turai zai yi kokarin shiga cikin shawarar ta wata sabuwar hanyar musamman."

Bugu da kari, Jean Juncker, shugaban hukumar zartaswar kungiyar EU ya bayyana cewa, Turai da Sin muhimman aminai ne, yana da matukar muhimmanci su tattauna bisa tushen nuna zaman daidai wa daida. Ya ce,

"Ina ganin cewa, ya kamata Sin da Turai su hada kai da juna wajen raya babban sha'ani. Domin mu kanmu da ma duniya, ya kamata mu amince da juna a maimakon nuna kiyaya da juna. Ina fatan bangarorin biyu za su cimma daidaito kan yarjejeniyar zuba jari ga juna, da kuma gaggauta kaddamar da aikin yiwa kungiyar WTO gyaran fuska tare da Sin." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China