in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Takardar bayani game da kare hakkin bil-Adam a Xinjiang
2019-03-28 08:42:41 cri

A ranar Litinin 18 ga watan Maris din shekarar 2019 ne, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da yaki da ta'adanci, tsattsauran ra'ayi da kare hakkin bil Adama a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar da ma irin ci gaban da yankin ya samu a fannoni daban-daban, inda ta zayyana kyawawan fasahohin yaki da ta'addanci a Xinjiang. Takardar ta kuma yi karin bayani kan matakan kawar da tsattsauran ra'ayi da kyautata dabarun mazauna wurin ta fuskar samun kudi da rayuwa. Kasar Sin na kokarin yin mu'amala da kasashen duniya a fannin yaki da ta'addanci.

Takardar ta yi wa kasashen duniya bayani kan muhimman matakai guda 3 da kasar Sin ta dauka wajen yaki da 'yan ta'adda, wato yin rigakafi, ware muhimman wuraren yaki da 'yan ta'adda, da hada kai da kasashen duniya.

Da farko dai, kasar Sin ta ba da muhimmanci ga yin rigakafin abkuwar aikace-aikacen ta'addanci, da hana kulla makarmashiyar kai harin ta'addanci,Kara samar da guraben ayyukan yi, ba da ilmin tilas tsakanin al'umma, ba da tabbacin kiwon lafiya da sauran matakan kyautata zaman rayuwar jama'a na daga muhimman matakan da kasar Sin ta dauka wajen yin rigakafin abkuwar aikace-aikacen ta'addanci.

Daga shekarar 2016 zuwa 2018, an kara samar da guraben aikin yi miliyan 1 da dubu 400 da dari 8 a jihar Xinjiang, mazauna yankunan karkara fiye da miliyan 8 da dubu 300 sun samu aikin yi a birane, sa'an nan kuma, an bullo da tsarin ba da ilmin tilas ga kananan yara a jihar, tare da ba da tabbacin kiwon lafiya ga dukkan al'umma a jihar.

Haka kuma bai kamata a alakanta aikin yakar ta'addanci da wasu wurare, ko wasu kabilu, ko kuma wasu addinai ba. Takardar ta kuma bayyana cewa, yayin da ake kokarin yaki da 'yan ta'adda, dole ne a girmama 'yancin bin addini, da al'adun kabilu, sannan kar a mai da wasu wurare, ko wasu al'ummomi, ko addinai saniyar ware.

Yanzu fiye da shekaru 2 ba a taba ganin abkuwar aikin ta'addanci ko sau daya a jihar Xinjiang ba, sa'an nan jama'ar jihar suna zama cikin kwanciyar hankali. A shekarar 2018, masu yawon shakatawa 'yan kasar Sin da na kasashen waje fiye da miliyan 150 sun ziyarci jihar Xinjiang, adadin da ya karu da kaso 40 bisa na shekarar 2017.

Yanzu mazauna yankin Xinjiang suna jin dadin zama da ma gudanar da ayyukansu, masu yawon shakatawa na gida da na waje, su ma ba su da wata fargaba a lokacin da suke yawon bude ido a yankin Xinjiang. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China