in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin mulkin Syria na al'ummar kasar ne in ji ministan wajen kasar
2019-03-18 09:59:51 cri
Ministan harkokin wajen kasar Syria ko Sham Walid al-Moallem, ya ce batun tsarin mulkin Syria na al'ummar kasar ne su kadai, bai kuma shafi wani bangare na daban ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SANA, ya rawaito Walid al-Moallem na bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin ganawar sa da jakadan MDD a Syria Geir Pedersen, wanda ya isa birnin Damascus da safiyar ranar ta Lahadi. Al-Moallem ya ce batun tsara kundin mulkin Syria ba ya bukatar tsoma bakin wasu kasashe na waje.

Mr. Geir Pedersen, ya isa birnin Damascus ne domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi shawo kan matsalolin siyasar kasar cikin ruwan sanyi.

Rahotanni sun ce, Al-Moallem da Mr. Pedersen sun tattauna game da dabarun siyasa da suka dace a bi, ciki hadda kafa kwamitin tsara kundin mulkin kasar, wanda zai yi nazari game da abubuwa dake kunshe cikin kundin mulkin kasar na yanzu.

A nasa tsokaci, Al-Moallem ya ce gwamnatin kasar mai ci ta yanke kudurin hada gwiwa da Mr. Pedersen, don tabbatar da cimma nasarar bukatar sa ta gudanar da al'amura bisa tsari.

A watan Janairun wannan shekara ne, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, babu wani wa'adin lokaci na kaddamar da kwamitin tsara kundin mulkin kasar ta Syria, ko da yake ya dace a gudanar da muhimmin aikin cikin gaggawa. Ya ce al'ummar Syria na bukatar kundin tsarin mulki madaidaici, wanda kuma daukacin al'ummar kasar za su amince da shi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China