Hukumar kula da harkokin gaggawa ta kasar ta bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin bada ceto, za kuma a gabatar da jerin sunayen mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin a lokaci mafi dacewa.
Masu bada ceto a wurin sun bayyana cewa, har zuwa yanzu akwai mutane fiye da 10 dake makale a baraguzan ginin, ciki har da dalibai a kalla 20.
Gwamnan jihar Lagos ya isa wurin abkuwar hadarin a yammacin jiya Laraba, inda ya bayyanawa 'yan jarida cewa, ginin shi ne mazaunin mutane ne, an kafa makarantar dake cikinsa ba bisa doka ba. Tuni dai aka bukaci rushe ginin bisa shirin gwamnati da aka gabatar, amma mai mallakar ginin ya ki amincewa da rushe shi. Ya zuwa yanzu, ba a tabbata dalilin da ya sa hadarin ya auku ba, amma gwamnatin jihar za ta yi bincike kan lamarin. (Zainab)