in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kara kokarin kyautata yanayin kasuwanci
2019-03-07 17:12:16 cri

A cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatarwa cikakken zaman na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13, wato hukumar koli ta mulkin kasar domin dubawa da kuma tattaunawa, an tanadi "sa kaimi kan kuzarin kasuwa, da dora muhimmanci kan kyautata yanayin kasuwanci" cikin manyan ayyukan gwamnati guda 10. Yayin da ake fuskantar sauye-sauye wajen yin ciniki a tsakanin kasa da kasa, kana kasar Sin na kyautata raya tattalin arizkinta yadda ya kamata, da ci gaba da kyautata muhallin kasuwanci yana amfanawa wajen kara kuzarin kasar Sin, da karfin yin takara ta fuskar tattalin arziki, haka kuma ya kasance kamar wata babbar dama ce ga masu zuba jari na duniya.

A cikin takardar mahukuntan kasar Sin, muhallin kasuwanci ya hada da yadda ake adalci a harkokin cinikayya, da yadda ake tafiyar da ayyukan gwamnati cikin gaskiya, da yadda ake yin adalci yayin da ake aiwatar da dokoki da manufofi, da kuma yadda ake bude kofa ga kowa da kowa. Tun bayan babban taro karo na 18 na JKS, kasar Sin ta dauki jerin matakan yin gyare-gyare a gida, don haka yanayin kasuwanci ya kyautatu. A cikin rahoton yanayin kasuwanci da Bankin Duniya ya kaddamar a watan Oktoban bara, ya daga matsayin kasar Sin zuwa ta 46, a maimakon ta 78. Yana ganin cewa, gyare-gyaren da kasar Sin ta yi cikin sauri a sassa daban daban sun baiwa mutane al'ajabi kuma suna da matukar amfani.

Yayin da ake kara fuskantar yanayi mai sarkakiya, kasar Sin za ta ci gaba da daukar wasu sabbin matakai don kyautata yanayin kasuwanci, a wani kokari na tinkarar kalubale ta hanyar kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Alal misali, Sin ta yi alkawarin rage jerin sana'o'i da ayyukan da za'a haramta zuba jari a kansu, da kara samar da sauki ga kamfanoni don su samu karin lokacin bunkasa sana'o'insu, tare kuma da aiwatar da shirin rage harajin da za'a biya da yawansu ya tasamma Yuan triliyan biyu. Wani abun da ya fi janyo hankalin jama'a shi ne, kasar Sin ta yi alkawarin nuna adalci ga kamfanoni daban-daban a fannoni da suka shafi ba su izinin gudanar da ayyuka da sayen kayayyaki da sauransu, a wani kokari na kirkiro wani yanayin kasuwanci dake nuna adalci ga kowane nau'in kamfani ko na kasar Sin ko kuma na ketare.

Yadda za a daidaita hulda a tsakanin gwamnati da kasuwa, da kara sassaucin shigar da baki 'yan kasuwa zuwa cikin kasuwarta, da kara sanya ido kan harkokin kasuwanci cikin adalci, da samar da yanayin kasuwanci mai sauki bisa doka, wani muhimmin aiki ne a gaban gwamnatin kasar Sin a bana. Dalilin da ya sa hakan shi ne saboda muddin kasuwa na da karfi, to za a iya tinkarar tabarbarewar tattalin arziki. Don haka, kasar Sin za ta kafa tsarin tantance aikin bada hidima da ma'aikatan gwamnatin za su yi, domin su bi ka'idoji da gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, za a himmatu wajen raya dangantakar kud da kud mai sabon salo a tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa, da ma kyautata tsarin tuntuba tsakanin gwamnati da kamfanoni, ta yadda ba ma kawai gwamnati za ta yi kokarin taimakawa kamfanoni wajen warware matsala ba ne, har ma za ta iya magance abkuwar musanyar iko da moriya, don haka 'yan kasuwa za su maida hankali kan raya aikinsu na kasuwanci ba tare da samun damuwa daga sauran fannoni ba.

Ta fuskar dokoki kuma, a matsayinta na babbar kasa ta biyu a fannin tattalin arziki, kasar Sin ta gaggauta hada kai da hukumomin dake tsara dokokin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da kara bude kofa da zartas da manufofi bisa dokar bai daya. A cikin daftarin dokar zuba jari na 'yan kasuwar kasashen ketare da aka gabatarwa taron wakilan jama'ar kasar Sin, an tabbatar da cewa, za a kiyaye 'yancin mallakar fasaha na masu zuba jari na kasashen ketare da kamfanoni masu jarin waje, kada a isar da fasaha ala tilas ta hanyar amfani da ikon mulki, hakan za a kawar da damuwar kamfanoni masu jarin waje a nan kasar Sin wajen neman ci gaba. Baya ga haka, kasar Sin na shirin ci gaba da rage sassan da baki ba za su zuba jari ba, tare kuma da amincewa da kamfanonin dake da dukkanin jarin waje su gudanar da ayyuka a fannoni mafiya yawa, da kyautata manufofin bude kasuwar takardu masu daraja da dai sauransu. Ko shakka babu, wadannan matakan za su nuna kyakkyawan fatan gwamnatin kasar Sin wajen bude kasuwa da kyautata muhallin gudanar da cinikayya.

Tare da kyautata yanayin yin ciniki, za a jawo karin mutane da kayayyaki da kuma jari, musamman yawan jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba, wanda aka dauke shi tamkar ma'aunin yanayin yin ciniki na kasashe da yankuna. Bisa halin raguwar jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba kai tsaye a bara, yawan jarin da Sin ta janyo ya karu, wanda ya zama matsayin koli a tarihi. Yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar Sin a bara ya kai dala biliyan 135, wanda bai hada da fannonin banki da hannayen jari da inshora ba, kuma yawansu ya karu da kashi 3 cikin dari. Yawan sabbin kamfanoni masu amfani da jarin waje a kasar ya karu da kashi 70 cikin dari. Wannan ya shaida cewa, dalilin da ya sa Sin ta ci gaba da zama kasa mafi kafa sabbin kamfanoni da jawo jarin waje a duniya, akwai babbar kasuwa dake da mutane kimanin biliyan 1 da miliyan 400 a kasar Sin, hatta ma Sin tana kyautata yanayin yin ciniki sannu a hankali.

Shugban kasar Sin Xi Jinping yana ganin cewa, ba zai yiwu ba a samar da yanayin kasuwanci mafi inganci, sai dai a kara kyautata shi kawai, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, yanayin kasuwancin kasar Sin bai kai sahun gaba a duniya ba tukuna, a don haka dole ne kasar Sin ta kara zurfafa yin gyaran fuska a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. An ce, a shekarar da ake ciki, gwamnatin kasar Sin za ta kara baiwa yankin gwajin ciniki maras shinge hakkin 'yanci wajen yin kirkire-kirkire, domin samar da goyon bayanta ga manyan yankunan raya tattalin arzikin kasar da na masana'antun fasahohin zamani da sauran sabbin yankunan da za a kafa. Duk wadannan matakai za su kara kyautata yanayin kasuwanci da kara habaka kasuwa, tare kuma da ingiza cudanyar tattalin arziki dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. Kasar Sin za ta kasance kasa mafi janyo hankalin 'yan kasuwa a fadin duniya baki daya. (Tasallah, Murtala, Kande, Bilkisu, Zainab, Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China