Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun saci wani babban jami'in gwamnati dake aiki a ofishin Gwamnan Buea, dake kudu maso yammacin kasar Kamaru, daya daga cikin yankunan kasar 2 dake da rinjayen masu amfani da Turanci, wanda kuma ke fama da rikici.
A cewar rundunar sojin kasar, 'yan bindigan sun saci Frankline Ngwa Che dake aiki a ofishin Gwamna dake kudu maso yammacin kasar ne da safiyar jiya Lahadi a gidansa.
Wata majiya daga rundunar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mutanen da suka sace shi sun nemi a ba su miliyoyin kudin CFA a matsayin kudin fansa.
Har ila yau a jiyan, hukumomi a yankin arewa maso yammacin kasar, wanda shi ma ke fama da rikici, sun ce an saci shugaban ma'aikatar kare muhalli na kasar.
A cewar majiyar ta rundunar sojin, da alama yanzu masu satar mutanen jami'an gwamnati suke hari.
Sace-sacen mutane na kara kamari a yankunan 2 na arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru, inda 'yan aware masu dauke da makamai ke neman kafa sabuwar kasa da ake kira da "Ambazonia". (Fa'iza Mustapha)