Darakta Janar na hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesusu, ya yi kira ga masu bada gudunmawa da su ci gaba da bada kudi domin shawo kan bazuwar cutar a kasar, ko kuma a samu komawa baya. A cewarsa, daga cikin dala miliyan 148 da abokan hulda masu aikin shawo kan cutar ke bukata cikin gaggawa domin ci gaba da gudanar da aikinsu, dala miliyan 10 kawai aka samu kawo yanzu.
A cewar wata sabuwar kididdiga da hukumar ta fitar, sama da mutane 80,000 a Jamhuriyar Demokadiyyar Congo ne aka yi wa rigakafi, sannan sama da mutane 400 sun samu kulawar lafiya. Har ila yau, an gano sama da mutane 40,000 da suka yi mu'amala da masu cutar, wadanda a kullum ake duba su tsawon makonni 3, domin tabbatar da su ma ba su kamu da rashin lafiya ba. (Fa'iza Mustapha)