A cikin rahotonsa na tsakiyar wannan wata, na tattarawa da yada bayanai game da yanayin rikice-rikice a fadin kasar, cibiyar ta gano wuraren da kai ya fuskantar barazanar tsaro a shiyyoyi 6 na kasar.
Shugban cibiyar Yusuf Anas, ya ce an gano wuraren ne bayan bitar al'amuran da suka faru a baya-bayan nan a wasu jihohi.
Jihohin da cibiyar ta bayyana sun hada da Kano da Kaduna da Kwara da Kogi da Adamawa da Taraba a shiyyar arewaci, sai kuma Lagos da Ogun da Rivers da Akwa Ibom da Anambra da Imo a shiyyar kudancin kasar.
Yusuf Anas ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da shugabannin al'umma da su shawarci mabiyansu game da kauracewa shiga duk wani abu da ka iya haddasa rikici da zai yi mummunan tasiri ga tsarin zaben. (Fa'iza Mustapha)