in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 11 sun mutu sakamakon harin da aka kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2019-02-17 16:45:09 cri

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta bayyana jiya Asabar cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hari a birnin Maiduguri, hedkwatar mulkin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 11.

Damian Chukwu, jami'in hukumar 'yan sandan Borno ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, da safiyar wancan ranar, dakarun sun kutsa kai cikin yankin, daga baya kuma sun yi harbi da bindiga kan jama'a, har ma 'yan kunar bakin wake su uku sun fasa tada abubuwan fashewa dake jikinsu.

Chukwu ya kara da cewa, harin ya haddasa mutuwar mazauna wurin 8, yayin wasu 15 suka jikkata, wadanda aka riga aka kai su asibiti. 'yan sanda da rundunar tsaro suna ci gaba da farautar wadanda suka aikata laifin a yankin.

Ana yawan samun hare-hare a wasu sassan Najeriya a 'yan kwanakin nan. A ranar 15 ga wata, wasu kauyukan dake jihar Kaduna sun gamu da hare-haren daga wasu maharani da ba'a san ko su wane ne ba suka kai, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane a kalla 66. A daren ranar 12 ga wata kuwa, an kai farmaki ga ayarin gwaman jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane uku.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China