Bisa sanarwar da ma'aikatar kudin Amurkar ta fitar, za ta hana amfani da dukiyoyin da wadannan kungiyoyi 2 da mutane 9 na Iran suka ajiye a kasar, sannan Amurkawa ba za su yi cinikayya da su ba.
A kuma wannan rana ne, jagoran kolin kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na intanet, inda ya bayyana cewa, ba zai yiwu a kawar da matsalolin da ke kasancewa tsakanin kasashen Iran da Amurka ta hanyar tattaunawa ba. Ya kuma ce, "Ba za a iya samun dabarar kawar da matsalolin dake akwai tsakanin Iran da Amurka ba. Haka kuma, ba za a iya samun kowane irin sakamako ba idan aka yi shawarwari da bangaren Amurka, in ban da asara da Iran za ta yi." Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya nanata cewa, a ganin Iran, kasar Amurka da wasu kasashen Turai masu zambo ne da ba su isa a amince da su ba. (Sanusi Chen)