in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a duba kididdigar tattalin arzikin Sin da nuna kyakkyawan fata gare ta
2019-01-21 19:56:47 cri

A ranar 21 ga wannan wata, an gabatar da kididdigar tattalin arzikin kasar Sin ta shekarar 2018, inda aka shaida cewa, yawan GDP na kasar Sin ya zarce biliyan dubu 90 karo na farko, wanda ya karu da kashi 6.6 cikin dari bisa na shekarar 2017, ta haka an cimma zaton da aka yi wato samun karuwa da kashi 6.5 cikin dari. Yawan CPI ya karu da kashi 2.1 cikin dari, wanda ya yi kasa da zaton da aka yi a wannan fanni wato kashi 3 cikin dari. An kara samar da sabbin ayyuka ga mutane miliyan 13 da dubu 610 a birane, yawansu ya zarce burin da aka tsara da kashi 23.7 cikin dari.

Yawan kudin shiga na kowane mutum a kasar ya kai kudin Sin yuan 28228, a hakika yawansu ya karu da kashi 6.5 cikin dari, wanda ya fi saurin bunkasuwar yawan GDP na kowane mutum a kasar. Kana yawan kudin kayayyakin da aka shiga da fitar ya zarce yuan biliyan dubu 30, wanda ya karu da kashi 9.7 cikin dari bisa na shekarar 2017, wanda ya zama matsayin koli bisa na lokacin da. Wadannan kididdigar tattalin arziki sun nuna cewa, kasar Sin ta cimma zaton da aka yi a farkon shekarar 2018 yadda ya kamata, an kiyaye sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Shekarar 2018, muhimmiyar shekara ce ga kasar Sin. A matsayin shekara ta farko da aka tabbatar da shirin raya kasa da aka tsara a gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19, ya kamata kasar Sin ta kara yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kara tinkarar hadarin raguwar raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da tsananta rikicin ciniki, da kuma yin kokarin tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata. Bisa yanayin da ake ciki, abun mai wuya ne kasar Sin ta iya cimma zaton da aka yi.

Game da yawan tattalin arzikin Sin, tun daga yawansu ya zarce biliyan dubu 10 a karo na farko a shekarar 2000, daga baya yawansu ya zarce biliyan dubu 70 a shekarar 2016, kana kuma yawansu ya zarce biliyan dubu 90 a shekarar 2018. Yawan tattalin arzikin Sin ya kiyaye samun karuwa, wannan ya shaida cewa, Sin tana da kyakkyawan tattalin arziki daga tushe.

Game da saurin bunkasuwar tattalin arziki, ko da yake saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin na shekarar 2018 wato kashi 6.6 cikin dari ya yi kasa da yawansu a shekarun baya baya nan, amma bai yi kasa sosai ba, ya dace da zaton da aka yi, da bukatun canja tsarin tattalin arziki daga samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri zuwa mai inganci. An yi nuni da cewa, wannan saurin ya kiyaye zama matsayin gaba na manyan kasashen dake da karfin tattalin arzikin duniya. Yawan gudummawar da Sin ta samarwa duniya a shekarar 2018 a fannin tattalin arziki ya zarce kashi 30 cikin dari, inda ta zama kasa mafi samar da gudummawar a duniya.

Samun koma baya dan kadan ya zama ruwan dare, yayin da ake raya tattalin arziki, abin da ya fi muhimmanci shi ne a fahimci yadda za a samu ci gaba cikin dogon lokaci. A watan Yulin bara, asusun ba da lamuni na duniya na IMF ya ba da rahoton shekara shekara kan tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2018, inda ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa sosai. Alkaluman da aka bayar a wannan karo kuwa ya shaida wannan ra'ayin na IMF.

A hakika dai, wasu alkaluman sun jawo hankalin mutane sosai, wadanda suka shaida ci gaban da tattalin arzikin kasar Sin ke samu yayin da yake kokarin kyautata tsarinsa. Alal misali, yawan kudin kashewa ya ba da gudummawa da yawanta ya kai 76.2% ga karuwar jimillar GDP, jimillar kudin da aka samu ta fannin sai da kayayyakin masarufi ta karu da 9% bisa ta shekarar 2017, ma'aunin Engel kuwa ya ragu da 0.9% bisa na shekarar 2017, duk wadannan sun shaida cewa, fannonin da Sinawa suka kashe kudi a kai sun samu kyautatuwa, kudin kashewa kuwa ya zama muhimmin karfi wajen sa kaimi ga karuwar tattalin arziki. Ban da wannan kuma, yawan jarin da sana'ar masana'antu ta samu daga gwamnati da masu zaman kansu ya karu sosai, wanda ya goyi bayan tattalin arzikin kasar sosai. Haka zalika, kasar Sin ta samu karuwa a fannin cinikin shige da fice da muhimman abokan cinikayya, a ciki yawan shigi da fici ga kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa ya karu da 13.3%, wanda saurinsa ya wuce na jimillar kudin kayayyakin shigi da fici da 3.6%, lamarin da ya nuna cewa, tsarin cinikayyar kasar Sin na samun kyautatuwa, wanda zai taimaka wajen warware rigingimun cinikayya. Game da kudin da aka samu wajen amfani da makamashi maras gurbata muhalli, yawansa ya karu da 1.3%, wanda ya taimaka wajen aiwatar da shirin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

Duk wadannan alkaluman sun nuna cewa, ko da halin da duk duniya ya kasance na da sarkakiya a shekarar 2018, amma tattalin arzikin kasar Sin na da karfi sosai wajen tinkarar hadari, har ma ya samu bunkasuwa yadda ya kamata, yayin da yake kokarin kyautata tsarin ci gabansa.

Bana ake cika shekaru 40 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kuma shekara ce mafi muhimmanci da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tabbatar da burinta na gina al'umma mai wadata a kasar, kana ana fuskantar yanayi maras tabbas a fadin duniya, a don haka gwamnatin kasar Sin ta gamu da kalubaloli da matsaloli iri daban daban, game da wannan, hukumar siyasa ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira taro a watan Disamban bara, inda aka bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu ya dace a tabbatar da daidaito a fannin samar da aikin yi, da na harkar kudi, da na cinikayyar waje, da na samun jarin waje, da na zuba jari da sauransu, ban da haka kuma, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauka cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan aikin tsara tsarin raya kasa, tare kuma da dauka matakan da suka dace, lamarin da ya nuna cewa, masu jagorancin jam'iyyar sun yi nazari sosai kan yanayin da ake ciki a halin yanzu.

Hukumar kididdigar kasar Sin ita ma ta amince da cewa, yanzu duk da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, amma akwai matsala dake gaban gwamnatin kasar, saboda muhallin ketare yana da sarkakiya, kila ne tattalin arzikin kasar Sin zai koma baya, a don haka kasar Sin tana sanya kokari matuka a fannoni biyar domin magance aukuwar hadari, misali kara kyautata tsarin tattalin arziki, da daga matsayin karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da kara zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, da hanzartar raya kasa ta hanyar kiyaye muhalli, da shiga tsarin gudanar da tattalin arzikin duniya.

Yayin taron tattauna kan aikin raya tattalin arziki da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira a karshen shekarar bara da ta gabata, an tabbatar da cewa, kasar Sin tana cikin kuma za ta ci gaba da kasance cikin lokaci mai muhimmanci wajen samun ci gaba, sakamakon da kasar Sin ta samu wajen ci gaban tattalin arziki ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba mai inganci sannu a hankali, ko shakka babu lamarin zai kara karfafa wa zuciyar Sinawa domin su kara nuna kwazo da himma kan aikin da suke yi a yau da kullum, haka kuma lamarin zai sa kasashen duniya su ci gaba da cike da imani ga makomar tattalin arzikin kasar Sin.(Kande Zainab Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China