in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin kayayyakin shige da fice na kasar Sin na shekarar 2018 ya kai Yuan fiye da biliyan dubu 30
2019-01-14 10:50:53 cri
Bisa kididdigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta gabatar a ranar 14 ga wata, an ce, yawan kudin kayayyakin shige da fice na kasar Sin na shekarar 2018 ya kai Yuan fiye da biliyan dubu 30.51, wanda ya zama matsayin koli a tarihi, kuma ya karu da kashi 9.7 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

A cikinsu, yawan kudin kayyayakin fice na kasar Sin ya kai Yuan biliyan dubu 16.42, wanda ya karu da kashi 7.1 cikin dari. Kana yawan kudin kayayyakin shige na kasar ya kai Yuan biliyan dubu 14.09, wanda ya karu da kashi 12.9 cikin dari.

Kididdigar ta kara shaida cewa, an ci gaba da inganta hadin gwiwar ciniki a tsakanin Sin da kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" a shekarar 2018. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China