Rahotanni sun bayyana cewa, an yi dauki ba dadi na tsawon lokaci, lokacin da mayakan kungiyar Hayat Tahrir al-Sham suka kaddamar da farmaki, kan wasu yankunan dake karkashin ikon dakarun "National Liberation Front" mai samun goyon bayan gwamnatin Turkiyya a wajen birnin Aleppo, inda dakarun na Hayat Tahrir al-Sham suka kwace iko da wasu garuruwa guda biyu.
A cewar kungiyar dake sa ido game da kare hakkokin bil Adama ta kasar, yara biyu sun rasa rayukansu yayin dauki ba dadin. Kaza lika mayakan wata kungiyar mai suna Ansar al-Din, sun yi yunkurin shiga tsakani cikin fadan, inda daga karshe suka dakatar da musayar wuta a yankin na yammacin Aleppo.
A wata Oktoba da ya gabata ma dai kungiyoyin dake adawa da juna a yammacin Aleppo, sun yi dauki ba dadi da juna, biyowa bayan kisan dakarun kungiyar Hayat Tahrir al-Sham da mayakan dake samun goyon bayan Turkiyya suka yi a arewacin kasar. (Saminu Hassan)