in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shekaru 40 da Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare
2018-12-20 13:37:50 cri

A safiyar ranar Talata ranar 18 ga watan Disamban shekarar 2018 ne, aka shirya wani babban taro a birnin Beijing, don murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam'iyya Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kwamitin soja na kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron da ma kusoshin gwamnatin kasar.

A tsakanin ranar 18 da ta 22 ga watan Disamban shekarar 1978 ne, aka shirya cikakken zama karo na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar, inda aka tsai da kudurin mai da hankali kan raya tattalin arziki, da aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida.

A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu sauyi daga tushe a dukkan fannoni. Inda matsakaicin jimillar GDPn kasar ya karu da 9.5 cikin 100 a kowace shekara, yayin da matsakaicin kudin shiga da jama'a ke samu ya ninka kusan dari 2, baya ga yadda yawan masu fama da talauci da ya ragu da miliyan 740, har ma yawan gudummawar da kasar Sin ta ba duniya ta fuskar tattalin arziki ya zarce kaso 30 cikin 100 a shekaru da dama a jere.

Bugu da kari, a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta bude kofarta ga waje don raya kanta, lamarin da ya sa jimillar cinikayyar shige da fice ta hajoji ta ninka har sau 198, yayin da jimillar cinikayyar shige da fice ta aikin ba da hidima ta ninka fiye da sau 147. Kaza lika yawan kudin waje da Sin ta jawo kuwa ya zarce dala biliyan 2000 gaba daya.

Yanzu haka kasar Sin ta zama kasa mafi girma ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki, kana kasar da ke sahun gaba ta fuskar masana'antu, kana kasa ta farko a fuskar cinikayyar hajoji, kuma mafi girma ta farko ta fuskar kudaden ajiyar ketare a duk duniya.

A cewar shugaba Xi, kasar Sin za ta nace ga raya manufar gurguzu mau halayyar Sin, da tunanin mazan jiya da suka kai ta ga samun tarin nasarori a fannoni daban-daban da nacewa ga inganta matakan tsaron kare kanta da kara inganta huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna da hakuri da juna da samun nasara tare.

Ya kuma jaddada cewa, dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 40 da suka gabata sun shaida cewa, shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne tushen tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin. Tsayawa kan jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin abu ne mafi muhimmanci wanda ba za'a iya canjawa ba ko kadan. Ya kamata a kare mutuncin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da tsayawa haikan kan shugabancinta yayin da kasar Sin take kokarin yin kwaskwarima da neman bunkasuwa, da raya harkokin cikin gida da na kasashen waje, da bunkasa harkokin tsaron gida da tafiyar da mulkin kasa da soja da sauransu.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi jam'iyyar kwaminis ta himmatu wajen inganta karfinta a fannonin tafiyar da harkokin mulki da shugabanci na-gari, ta yadda za'a bi hanya madaidaiciya, wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Masana na cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 40 da suka gabata, wani sakamako da ba a taba ganin irinsa a tarihin bil-Adam ba. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China