Rahoton mai taken "nasarar da aka samu wajen kare hakkokin bil'adama cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin" ya ce manufar ta taimaka wajen 'yantarwa da samar da ci gaban ma'aikata a cikin al'umma, sannan ya bude wani sabon babi ga ra'ayin gurguzu mai halayyar musammam ta kasar Sin, da kuma ci gaban hakkokin bil adama.
Ya ce cikin shekaru 40, al'ummar Sinawa sun yi aiki tukuru karkashin shugabanci mai karfi na JKS, kuma an samu manyan sauye-sauye baya ga ingantuwar yanayin zaman rayuwa.
Rahoton ya kara da cewa, a ko da yaushe, JKS kan ba bukatu da muradun jama'a muhimmanci, da tabbatar da mutane sun aiwatar da gyare-gyare da kansu, domin su ci gajiyarsu tare.
Har ila yau, rahoton ya ce kasar Sin ta gudanar da tarin musaya da hadin gwiwa dangane da kare hakkokin bil'adama, kuma ta kiyaye hakkokin bil'adama na kasa da kasa da suka wajaba a kanta. (Fa'iza Mustapha)