Bisa yadda aka tsara, taron zai amince da yarjejeniyar da aka cimma kan batun kaura a hukumance, wadda kasashe mambobin majalisar suka fara amincewa da ita a ranar 13 ga watan Yulin.
A cewar MDD, yarjejeniyar cikakken daftari ne da ya kunshi yadda za a lura da batun kaura a duniya, da yadda za a shawo kan kalubalenta da karfafa hakkokin masu kaura da kuma bada gudunmuwa ga samun ci gaba mai dorewa.
Wannan ita ce yarjejeniya ta farko da aka tsara karkashin inuwar MDD, domin ta mamaye kowanne bangare na batun kaura a duniya bisa yanayin da ya dace. (Fa'iza Mustapha)