in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron G20 na Argentina
2018-12-06 09:46:38 cri

A kwanakin baya ne aka rufe taron koli na G20 a Bounes Aires, babban birnin kasar Argentina. An cimma muhimman sakamako masu yawa da kuma matsaya daya a tsakanin kasashe daban daban a fannoni da dama a yayin taron, batutuwan da suka samu jinjina da amincewa sosai daga kasashen duniya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabinsa a yayin taron kolin na G20 cewa, shugabanni da manyan jami'an kasashe membobin kungiyar G20, da kungiyoyin kasa da kasa, sun yi musayar ra'ayi sosai kan ayyukan kirkiro sabbin fasahohi, da gudanar da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, domin tattaunawa kan shirin raya tattalin arzikin duniya.

Masana na nuna cewa, an gudanar da taron kolin G20 karo na 13 na kasar Argentina a yayin da tattalin arzikin duniya ke fama da rashin tabbas, biyo bayan takaddamar cinikayya da ta kunno kai tsakanin Sin da Amurka, manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, da karin ba da kariya ga harkokin cinikayya da daukar ra'ayin kashin kai da sauransu da kuma kokarin ganin an aiwatar da gyare-gyare kan kungiyar ta G20.

Mahalarta taron kolin G20 sun tsara shirin bunkasuwar cinikayya a duniya, kana za a ci gaba da goyon bayan tsarin cinikayya a tsakanin kasashe daban daban, da kuma nanata alkawarin nuna adawa da ba da kariya ga harkokin cinikayya. Ana sa ran tattalin arzikin duniya zai samu farfadowa ta hanyar inganta cinikayya da zuba jari a duniya.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi farin ciki kan yadda shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, suka cimma daidaito kan batutuwan da suka hada da ra'ayin sanya bangarori daban daban su shiga a dama da su, da yunkurin neman ci gaba mai dorewa, da aikin tinkarar sauyin yanayin duniya, da makamantansu.

A cewar mista Guterres, sanarwar da aka gabatar a karshen taron G20, ta shaida yadda shugabannin kasashe mambobin G20 suka lura da muhimmancin yin amfani da manufar da ta kunshi ra'ayoyin bangarori daban daban wajen daidaita al'amura a fannin ciniki, gami da yin kwaskwarima kan kungiyar ciniki ta duniya WTO.

Haka zalika shugabannin sun nanata alkawarinsu na ci gaba da bin tsarin duniya da aka kafa bisa ka'idojin kasa da kasa.

Masu fashin baki na cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an cimma nasarar wannan taron kuma za a ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron, domin tabbatar da neman samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China